Babu auren jinsi a yarjejeniar Samoa —Kungiyar Lauyoyi

Kungiyar ta ce yarjejeniyar Samoa da ake surutu a kai bai ba ta da wata alaka da batun auren jinsi

Babu auren jinsi a yarjejeniar Samoa —Kungiyar Lauyoyi

Jakadan Najeriya a kasar Belgium, Obinna Onowu, tare da wakilan Kungiyar EU, a lokacin rattaba hannun kan yarjejeniyar Samoa a birnin Luxembourg. (Hoto: OACPS/X)

Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta ce Yarjejeniyar Samoa da gwamnatin kasar ta sa hannu a kai ba ta da wata alaka da auren jinsi da ake cece-kuce a kai.

Shugaban NBA, Yakubu Maikyau, ya ce kungiyar na da hannu wajen sanya hannu kan yarjejeniyar Samoa kuma babu wani bangare na yarjejeniyar da ke da alaka da ’yan luwadi da madigo, ko auren jinsi (LGBTQ).

Shugaban na NBA ya ce kungiyar ta lura da ce-ce-ku-cen da ake a Najeriya kan rattaba hannu da kasar ta yi kan yarjejeniyar Samoa wanda ake zargin an shardanta mata amincewa da karewa ko yarda da haƙƙoƙin LGBTQ, don samun rancen kudi Dala biliyan 150.

Maikyau, a cikin wata sanarwa a safiyar Talata, ya ce, “Babu wani tanadi a Yarjejeniyar Samoa da ke bukatar Najeriya ta amince da ’yan luwadi ko auren jinsi a matsayin sharadin samun rancen Dalar biliyan 150.

“Maimakon haka, yarjejeniyar ta amince ta kasance a karkashin dokokin kasar da kuma ikon kasar na cin gashin kai.

“Wato Yarjejeniyar Samoa ta amince, misali, da dokar haramcin auren jinsi ta Najeriya ta 2023 da kuma ikon kundin tsarin mulkin Najeriya  na 1999.”

Ya kara da cewa da akwai wani tanadin yarjejeniyar da ya saba wa dokokin Najeriya da kungiyar ta shawarci gwamnati kada ta sanya hannu.

Da yake shawartar ’yan Najeriya da su kasance masu taka-tsan-tsan, Shugaban na NBA ya ce kungiyar na sa ido kan ayyukan gwamnati tare da yin tsayuwar daka wajen kare al’umma a kowane lokaci.