Babu bambanci tsakanin mulkin PDP da na soja –Dokta Lame
Dokta Ibrahim Yakubu Lame, gogaggen malami ne kuma ma’aikacin gwamnati da ya tsunduma cikin harkokin siyasa a lokacin shirin mayar da mulki a hannun farar hula na 1992 inda ya lashe zaben Sanatan Bauchi ta Kudu a karkashin Jam’iyyar NRC. Kuma ya yi mashawarcin Shugaban kasa da Ministan Harkokin ’Yan sanda a karkashin gwamnatin PDP. […]
Dokta Ibrahim Yakubu Lame, gogaggen malami ne kuma ma’aikacin gwamnati da ya tsunduma cikin harkokin siyasa a lokacin shirin mayar da mulki a hannun farar hula na 1992 inda ya lashe zaben Sanatan Bauchi ta Kudu a karkashin Jam’iyyar NRC. Kuma ya yi mashawarcin Shugaban kasa da Ministan Harkokin ’Yan sanda a karkashin gwamnatin PDP. Tsohon jigon na Jam’iyyar PDP wanda yanzu jigo ne a sabuwar Jam’iyyar APC, ya ce suna fafutikar kawar da Jam’iyyar PDP daga mulki ne saboda babu bambanci a tsakanin mulkin PDP da na soja shekaru da yawa bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a kasar nan:
Daga Mu’azu Hardawa, Bauchi
Aminiya: Yallabai, mene ne takaitaccen tarihinka a siyasance?
Dokta Lame: Bayan na yi aiki da gwamnatin jihata Jihar Bauchi na koma aiki da Gwamnatin Tarayya inda na zamo Babban Darakta a Hukumar Kogin Hadeja/Jama’are, daga nan aka kira ni na dawo na shiga siyasa na zama Sanata a Jam’iyyar NRC. Bayan rusa harkokin siyasa sai jna koma na ci gaba da aikina a makaranta daga nan na shiga aikin al’umma na kafa kungiyar Bauchi Forum da ta kunshi matasa da masu ilimi don harkar gina kasa, har muka dawo muka shiga Jam’iyyar PDP. Ni ne Sakatarenta na farko har Allah Ya sa muka kafa gwamnati na yi mai bada shawara ga Shugaban kasa na yi Darakta Janar na yi Ministan ’Yan sanda daga nan na bar PDP na koma Jam’iyyar ACN yanzu na dawo muna gwagwarmayar kafa Jam’iyyar APC, kuma a yanzu ni ne Sakataren Shirya Hadaka da sauran jam’iyyun adawa.
Aminiya: Me ya yi zafi ka bar PDP duk da kokarin kafata da kuka yi?
Dokta Lame: Akwai abubuwan da suka auku, saboda an gina PDP kan manufofin niyyar sauya yanayin siyasar Najeriya wanda zai kawo ci gaba, saboda la’akari da shekarun da soja suka yi suna mulki, don haka muka ga akwai bukatar kowa ya zo a kawo sauyin. Da wannan akida muka shiga, amma kwarewar soja a mulki sai suka ga akwai hadari su bar mulki ya fita a hannunsu don haka suka dawo ta wata hanya suka shiga suka kame mulkin ta hanyar ba Obasanjo mulkin kasa suka zuba mutanensu a gaba. Tun daga taron PDP na Jos suka wargaza dukkan manufofin PDP, ya zamo dimoruradiyya babu ita ana tafiya ne irin na tsarin mulkin soja, na shugabanni su ne wuka su ne nama, babu batun ba kowa hakkinsa, ba bambanci tsakanin majalisa da sashin zartarwa, gwamnoni da Shugaban kasa sun zamo su ne komai, ba a yin zabe a cikin jam’iyya. Sai ya zamo an koma mulkin kama-karya ba mulkin da zai kawo ci gaba ba. Mun lura tsawon lokaci kasar tana ta rikice, abin da ya dace a gina ya taimaki jama’a ba a yin sa, jama’a kuma ba su da bakin magana, saboda an kawar da dimokuradiyya ba a ba mutane damar su yi magana. Daga nan mutane suka lura ba inda za su shiga su samu arziki su samu daukaka da karfi, sai siyasa, don haka ’yan kasuwa aminan soja da sojojin suka zamo masu tara kudi su shiga jam’iyyar da karfi su amshi mulki su ci gaba da kasuwancin su da kwashe dukiyar kasa. PDP ta zamo babban kamfanin Jari-Hujja na wadanda suke son su yi kudi dare daya a Najeriya. Don haka ta kashe dukkan cibiyoyi da ya kamata jama’a su yi amfani da su don gina kasa. Ilimi da doka da hanyoyin inganta jin dadin jama’a da walwala duk an karya su, mutane sun zamo ba sa iya dogaro da rayuwa ba a jikin gwamnati ba, komai ya yi wahala, dukiya na hannun kalilan din mutane. Ba irin kokarin da ba mu yi ba don mu sauya tafiyar amma lamarin ya gagara, an yi wa kasar da gwamnatin mummunan rauni. Don haka irinmu-irinmu da muke ta kokarin tashi tsaye mu amshe mulkin a siyasance abin ya gagara, saboda haka muka sake shawarar duk ’yan hamayya su watsar da jam’iyyunsu a hada karfi wuri daya don a yaki wadannan mutane tun kafin su wargaza mana kasa, wacce da karfi da yaji an mayar da kowa talaka.
Muna zaune cikin mulkin danniya da wahala, an kanainaye kowa a Najeriya an hada rigingimun addini da na kabilanci, an shigar da mu cikin mawuyacin hali da gangan, ana ta sace dukiyar kasa, gwamnati ta zamo bata da alkibla, don haka yanzu muka kafa APC don mu hade wuri daya mu tunkari wadannan mutane a samu sauyi da ci gaba mai amfani ga kasar nan ta hanyar tunkarar duk wani kalubale na ’yan Jari-Hujja masu sace dukiyarmu suna lalata kasa. Da haka ne za mu dawo da martabar wannan kasa da ta mutanenta a idon duniya, wahalar da ake fuskanta ta kau kowa ya san yana cikin kasa ce da Allah Ya yi mata albarka. Saboda halin da ake ciki ana yaki a wasu sassan kasa kowane mutum ko mene ne addininsa ko kabilarsa a kowane wuri yake yana shan wahala kuma yana fuskantar matsalar rayuwa.
Aminiya: Dokta, na ga alama tun kuna cikin gwamnatin PDP kun hangi wannan matsala, me kuka yi don sauya lamarin, kuma mene ne kiranka ga jama’ar kasa a kan shirinku na yanzu?
Dokta Lame: Kirana ga dukkan ’yan Najeriya shi ne, su gane cewa a tarihin duniya kowace al’umma na shiga cikin irin wannan matsala, kuma mutane su ne suke tunani da gyara tsarinsu, su daure wajen sadaukar da kai don su gyara makomarsu, Allah Ya ce tashi in taimake ka, dole mu tashi da niyyar alheri. Jama’ar Najeriya su gane cewa wannan yanayi da ake ciki yana da hadari, kuma yana iya kawo halaka, idan aka bar shi zai wargaza rayuwar kowa a kasar nan. Don haka a ba jam’iyya ta APC goyon baya kuma a tabbatar an bi ka’idojinta ta hanyar fito da shugabanni nagari da za su taimaka wajen gyara abubuwan da suka lalace, ba kurum don mutum yana da kudi ko ya san wani a ba shi jagoranci ba. A duba a ga wadannda suka san abin da ya lalace suna da kwarewa da halin iya kawo gyara kan halin da ake ciki a shugabantar da su. A sani ’yan Jari-Hujja suka kashe PDP, wadanda suka san cewa hanyar samun kudi shi ne kurum a shiga gwamnati. Su ne masu fito da kudi su tara jama’a su ba su sai su kuma su ce sai su.
Aminiya: Wace shawara za ka ba ’yan Arewa don su gyara siyasarsu kamar yadda Yarabawa suke yi su samu nasara?
Dokta Lame: Ba tsafi suke yi ba don samun nasara, sai yarda da wasu mutane daga cikinsu da suka yi suka ba su amana, su kuma suka dauka kamar yadda ake tsara su. Don haka mu ma a Arewa mu fitar da mutane nagari mu yarda da su da irin shawarar da za su ba mu, mu yi imanin sun yarda da matsalarmu kuma za su iya yin wani abu a kai. Yanzu hadin kan da muke yi da yankin Yarabawan muke yi, sun yarda da mu, mun yarda da su, don haka muke koyi da tsarinsu na dukkan jihohinsu da yadda suke hada kai suke gudanar da hidimomin su. Mu sani abin da ya shafi mutumin Bauchi ya shafi na Borno abin da ya shafi na Yobe ya shafi na Kano, don haka yanzu muke son tun daga shiyyar Arewa maso Gabas mu fara dunkulewa kamar yadda Yarbawa suka yi kafin su ma sauran shiyyoyin su dunkule sai mu hadu wuri daya mu kawo sauyi, insha Allah saboda duk matsalarmu daya ce.
Sannan mutanen Najeriya su lura kada su sake bayar da mulki ga wadanda ba su sani ba, don dan abin da za su ba su, idan an ba su su karba dama hakkinsu ne, amma su yi abin da ya dace, su zabi wanda zai kai su tudun mun-tsira. Ana bayar da mulki ne ga mutanen kwarai da aka san su aka san halinsu da irin tausayi da taimakon da suka yi a baya, shi zai fitar da mu daga wannan matsala da muke ciki. Amma idan kuka amshi kudi kuka dauki mulki kuka ba mutane don dan abin da suka ba ku, wanda ba zai kashe muku yunwa da kishirwa ba, to hadarin da muke ciki yanzu kamar wasan yara ne a kan wanda za a shiga a gaba Allah ya sauwaka.
Ba wanda a duniya ya ce sai gwamnati ce za ta magance matsalolin mutane, yanzu kamar lantarki idan jihohin Arewa maso Gabas suka hadu za su iya gina tashar da za ta samar da haske ga Arewa. Idan ba mu da mai, sai mu gina noma mu kawo abin da zai amfanemu, kada mu zauna ana ba mu kudi muna cinyewa ana zaginmu, dole mu nemo abokan hulda a duniya don mu ci gaba. Rashin tsaron da ke damunmu idan mun hada kai zai kau insha Allah.
Aminiya: Ta yaya za a cire siyasar bambancin addini da kabilanci a Arewa:
Dokta Lame: Babu abu mai kyau kamar addini, Allah Ya tsara kowa kan addininsa da umarnin ya tsaida adalci ga kowa a rayuwa, abin da ake yi yanzu matsala ce da siyasar PDP ta kawo don a samu damar mulki irin na Jari-Hujja shi ya sa ake ta kashe juna. Wannan ya sa muke nuna wa mutane kowa ya bi tsari, ya bi doka ya tsaya kan adalci a yi abin da zai gina siyasa mai kyau a kasa. Mutane su fahimci muna son kawo gyara na gaggawa mai muhimmanci, don haka dole a yi hakuri a samu shugabannin da za su iya fitar da mu daga wannan matsala. A bar siyasar gaba ko nuna bambancin addini ko kabilanci. Kowa addininsa ya umarce shi ya zamo na kwarai, ya zamo mai tausayi da rike amana ya so wa dan uwansa abin da ya so ga kansa, ba addinin da ya koyar da gaba sai zaman adalci da rike amana da gaskiya. Mu bar siyasar kudi mu guji mabarnata masu siyasar kudi, mu nisanci masu sace dukiya su kawo suna raba mana ita, don su sake tara wata, mu yi wa kanmu kiyamullaili.
Mutanen Bauchi kuma kirana gare su shi ne su hada kai, akidarmu ta ba mu haske mu bar maganar neman matsayi mu gina jam’iyya don ta cire mu daga cikin mawuyacin halin da muka samu kanmu, da fatar Allah Ya wuce mana gaba.