Babu barazanar da za ta hana mu fitar da sunayen barayin gwamnati-Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ce babu irin takurawa ko barazanar da za ta dakatar da ita fitar da karin sunayen barayin da ake zargi da satar kudin gwamnati. Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar jiya ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, […]

Gwamnatin Tarayya ta ce babu irin takurawa ko barazanar da za ta dakatar da ita fitar da karin sunayen barayin da ake zargi da satar kudin gwamnati.
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar jiya ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Segun Adeyemi.
Alhaji Lai Mohammed ya ce tun lokacin da gwamnatin ta fitar da jerin sunayen wadanda ake zargi sun saci kudin gwamnati kashi na biyu an rika samun yunkurin yi wa gwamnati barazana don kada ta fitar da karin sunayen.
Alhaji Lai Mohammed ya ce tun lokacin da gwamnatin ta fitar da jerin sunayen wadanda ake zargi sun saci gwamnati kasha na biyu an rika samun yunkurin yi wa gwamnati barazana don kada ta fitar da karin sunayen.
“Marubuta na bogi sun rika tura rubuce-rubuce don su bata sunan gwamnatin tarayya ta kafar sadarwa da dandalin sada zumunta. Mafiyawan marubutan sun zargi gwamnati da siyasantar da lamarin yaki da cin hanci saboda fitar da sunayen da ta yi. Amma mu mun musanta zargin da suka yi”. Inji shi.