Babu batun karba-karba a kujerar Gwamnan Filato – Gwamna Jang

Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang ya ce babu tsarin karba-karba, a kan kujerar Gwamnan Jihar Filato. Gwamna Jang ya bayyana haka ne a lokacin da yake rantsar da wasu sababbin kwamishinonin jihar guda hudu a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Jos. Gwamna Jonah Jang ya ci gaba da cewa, “Wasu da suke takarar kujerar […]

Babu batun karba-karba a kujerar Gwamnan Filato – Gwamna Jang
Babu batun karba-karba a kujerar Gwamnan Filato – Gwamna Jang

Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang ya ce babu tsarin karba-karba, a kan kujerar Gwamnan Jihar Filato. Gwamna Jang ya bayyana haka ne a lokacin da yake rantsar da wasu sababbin kwamishinonin jihar guda hudu a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Jos.

Gwamna Jonah Jang ya ci gaba da cewa, “Wasu da suke takarar kujerar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP, sun kai karata a Abuja, cewa wai na hana kowa ya fito takara, saboda ina son na baiwa dan kabilar Berom takarar Gwamnan Jihar Filato. To ina son in tabbatar da gaskiyar magana cewa babu tsarin karba-karba a kan kujerar Gwamnan Jihar Filato. Don haka kowane dan Jihar Filato yana da damar ya fito ya nemi kujerar Gwamnan jihar.”
Gwamna Jang ya ce saboda haka wasu ’yan takarar kujerar Gwamnan sun fito daga kudancin jihar wasu sun fito daga yankin tsakiyar jihar, wasu kuma sun fito daga yankin arewacin jihar.
Ya ce “Ina son in tunatar da al’ummar Jihar Filato cewa ba Jonah Jang ne zai sanya wanda zai gaje shi ba, Allah ne zai bai wa wanda zai gaji Jonah Jang mulkin Jihar Filato.”
Gwamnan Jang ya ce ya kamata masu son kujerar Gwamnan Jihar Filato su bi al’ummar jihar su bayyana musu irin abubuwan da za su yi musu na ci gaba idan suka samu nasara, maimakon su buge da zuwa Abuja suna neman kujerar Gwamnan. Ya ce Abuja ba za ta zo ta zabi Gwamnan Jihar Filato ba.
Ya ce idan kana mutum yana son tsayawa takarar Gwamna ko kujerar Sanata ko dan Majalisar Tarayya, ya zo ya nema a wajen al’ummar jihar, ya bayyana musu manufofinsa, maimakon ya tafi Abuja yana nema. “Allah ne Yake bayar da mulki ga wanda Ya so, idan Allah Ya yi nufin
ba ka mulki babu wani mutum da ya isa ya hana,” inji shi.
Da ya juya ga kwamishinonin da ya rantsar kuwa Gwamna Jang ya ce an nada su ne don cike gurbin tsofaffin kwamishinonin da suka sauka a kwanakin baya.
Ya ce sababbin kwamishinoni sun zo a wani yanayi na kammala wa’adin wannan gwamnati, don haka ya yi kira a gare su kan su tsaya su sadaukar da kansu wajen gudanar ayyukansu domin a samu nasara.
Sababbin kwamishinonin da aka rantsar sun hada da Alhaji Abubakar Muhammad Kwamishinan Watsa Labarai da Injiniya Gyang Tanko Kwamishinan Ayyuka da Mista Chris Kwaja Kwamishinan Ma’aikatar kananan Hukumomi da Masarautu da Injiniya Arings bincent Yaki, Kwamishinan Ruwa.