Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda
Tsarin rajistar motocin da ake kira e-CMR zai taimaka wajen inganta aikin jami’an ’yan sanda
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a yanzu babu buƙatar jami’anta su riƙa tare motoci suna duba takardu bayan fito da tsarin rajistar bayanan motoci na yanar gizo.
Mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba.
- ‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu
- A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu
Adejobi ya ƙara da cewa da zarar tsarin rajistar motocin na e-CMR ya fara aiki, masu motoci ba sai sun zo a tantance takardunsu da kansu ba, domin za a tattara bayanan motoci baki ɗaya a yanar gizo.
“Za a daina tsayar da motoci ana duba takardunsu — an horar da jami’anmu amfani da fasahar zamani wajen tantance takardun,” kamar yadda ya bayyana a X.
“Ta hanyar amfani da tsarin na E-CMR, ba sai ka je tantance takardun motarka da kanka ba. Za ka iya yin hakan ta intanet cikin sauri da sauƙi.
“Idan ka yi rajistar motarka a tsarin NPF E-CMR, sai aka sace ta, dandanan za ka shiga intanet ka nuna motar a matsayin wadda aka sace domin a kama wanda yake ciki.”
Ya ce da zarar ka kunna alamar sace motar a intanet, jami’an ’yan sanda a faɗin ƙasar za su ji cikin ’yan daƙiƙa kaɗan, wanda hakan zai sauƙaƙa wajen gano motar.
Tun a watan Yulin da ya gabata ne Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa za ta fara amfani da fasahar zamani wajen yi wa motoci a ƙasar nan rajista.
Rundunar ta ce sabon tsarin mai amfani da na’urorin zamani, zai fara aiki domin inganta tsaro a sassan ƙasar.
Adejobi ya ce sabon tsarin da Babban Sufeton ’Yan sanda, Kayode Egbetokun ya kawo na da nufin daƙile matsalar tsaro kama daga satar ababen hawa da fashi da makami.
Ya ce tsarin rajistar motocin wanda aka yi wa laƙabi da e-CMR zai taimaka wajen inganta aikin jami’an ’yan sanda wajen gudanar da bincike da daƙile aikata laifuka ta amfani da ababen hawa, har ma da ayyukan ’yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce sabon tsarin rijistar ababen hawan zai riƙa amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan kai tsaye na ababen hawa da waɗanda suka mallake su da kuma ayyukan da suke yi da su.
Hakan na nufin daga lokacin fara aiki da wannan sabon tsari, duk wasu sauye-sauye na takardun mota ko kuma wasu sassan motar za su gudana cikin sauƙi ba kamar yadda a baya ake ɗaukar lokacin haɗa irin waɗannan takardu ba.