Babu Dalilin Ci Gaba Da Rabon Tallafin Abinci —Gwamnan Gombe

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya ce, duk wanda ba zai yi noma ba ya hakura

Babu Dalilin Ci Gaba Da Rabon Tallafin Abinci —Gwamnan Gombe

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya ce, duk wanda ba zai yi noma ba ya hakura, domin babu dalilin mutane su zauna a ci gaba da ba su tallafin abinci.

Gwamna cikin fushi ya ce ya kamata kowa ya koma gona ya ciyar da kansa, saboda babu dalilin da gwamnati za ta ci gaba da ba da tallafin abinci.

A cewarsa, ya riga ya rufe kofar bayar da tallafin abinci a Jihar Gombe, idan mutane sun shirya su koma gona, zai sama musu takin zamani, amma tallafi kam, ba zai sake bayarwa ba.

Ya ce sauran shinkafa da taliyar tallafi da suka rage a ajiye kuma, makarantun gwamnati zai raba wa, domin an wuce lokacin ci gaba da bai wa mutane tallafi.

Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne a wajen bikin bude wani sabon kamfanin takin zamani a Gombe.

Ya bayyana cewa ya umarci Kwamishinan Aikin Gona umurnin sayen ton 2,000 na taki daga kamfanin; kuma kafin karshen watan nan na Mayu zai kaddamar da taki idan har jama’a sun shirya yin noman.

A cewarsa, zai samar da takin ne domin ya kure gudun makaryata, idan kuma suka ki yin noma, to kada su zargi gwamnati da cewa ba ta kawo musu taki ko tallafi ba, duk wanda ba zai yi noma ba ya hakura.

Daga nan yace duk wata hikima da zai yi amfani da duk wata hikima wajen tallafa wa harkar noma, amma dai batun a ci gaba da raba tallafin abinci a Gombe Gombe, an yi na karshe.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji