Babu dalilin gaba a tsakanin Musulmi da Kirista – Sheikh dahiru Bauchi
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce babu gaba a tsakanin Musulmi da Kiristan kasar nan don haka ya bukaci su zauna lafiya da junansu.Sheikh dahiru Bauci ya bayyana haka ne lokacin da wasu fastoci na kungiyar samar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da Kirista a karkashin shugabancin Fasto Yohanna […]
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce babu gaba a tsakanin Musulmi da Kiristan kasar nan don haka ya bukaci su zauna lafiya da junansu.
Sheikh dahiru Bauci ya bayyana haka ne lokacin da wasu fastoci na kungiyar samar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da Kirista a karkashin shugabancin Fasto Yohanna Buru da Barista Solomon Dalung suka kai je yin buda-baki a gidansa da ke Kaduna.
Sheikh dahiru Bauchi ya ce, “Babu gaba a tsakanin Musulmi da Kirista, addinin Kirista addini ne na tausayi, addinin Musulunci kuma addini ne na zaman lafiya. To, mai addinin tausayi ai zai zauna lafiya da kowa ballantana mai addinin zaman lafiya. Mai addinin zaman lafiya kuma zai iya zama da kowa, balle mai addinin tausayi. Saboda haka, me ya kawo gaba ko fada? Idan ka ga Musulmi da Kirista suna fada sai dai wani abu daban, amma ba saboda addini ba.”
Shehin Malamin ya kara da cewa: “Ba za mu manta da abin da Kiristoci suka yi mana a zamanin Annabi Muhammad (SAW) ba, lokacin da makiyansa na Makka suka hana shi walwala inda hakan ya sa ya tura sahabbansa zuwa Habasha domin neman kariya. Suka kuma zauna can lafiya ba tare da tsangwama ba. Saboda haka alherin da Kiristoci suka yi mana, ba za mu manta da shi ba, Muna rike da wannan zumunta. Hakika duk inda Musulmi yake ya yi imani da Manzon Allah, kuma yadda ya yi imani da Annabi haka ya yi imani da Annabi Isa. Saboda haka babu wani gaba a tsakaninmu. Masoyin masoyi ba makiyi ba ne saboda haka son masoyi soyayya ne. Don haka akwai bukatar Musulmi da Kirista su koma irin zumuntan da aka san su da ita a baya. Allah na da ikon Ya cika wannan kasa baki daya da Musulmi babu Kirista ko ya cika kasar nan da Kirista amma sai Ya hada mu domin ya gaurayamu don ya jarraba mu ya ga ko za mu yarda da ikonSa ko ba za mu yarda ba.”
Sheikh dahiru Bauchi ya ce: “Mun yarda da ikon Allah da Ya hada mu, kasarmu ce gaba daya babu mai korar wani, ko hana wani walwala ko yin addininsa. Muna kira ga shugabanni su yi adalci domin a samu zaman lafiya. Akwai matasa da yawa marasa aiki a kasar nan.”
Barista Dalung da Fasto Yohanna Buru sun ziyarci malamin ne a kokarinsu na neman hadin kai a tsakain Musulmi da Kiristan kasar nan.