Babu dalilin gaggauta yanke shawara kan makomata — Ronaldo
Saboda haka zan bar wannan gasa cikin kwanciyar hankali. Na yi iyakar ƙoƙarina, kuma rayuwa za ta ci gaba.
Tauraron ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya ce ba zai yi gaggawar yanke shawara kan makomarsa ba bayan ƙasarsa ta fice daga Gasar Kofin Duniya sakamakon rashin nasara da ci 1-0 a hannun Spain a wasan zagaye ’yan 16.
Ronaldo mai shekara 41 ya bayyana tun kafin wasan cewa wannan ce Gasar Kofin Duniya ta ƙarshe da zai buga.
- Iran ta harba makamai masu linzami kan jiragen ruwa a Mashigar Hormuz
- Hamas ta rusa gwamnatinta da ke mulkin Gaza kusan shekara 20
Da aka tambaye shi bayan wasan abin da zai biyo baya, Ronaldo ya ce zai ɗauki lokaci kafin ya yanke hukunci.
“Eh, wannan ce Gasar Kofin Duniya ta ƙarshe da zan buga. Amma zan samu lokaci na yi tunani game da sauran abubuwan da ke gaba, in kasance tare da iyalina, ba tare da gaggauta yanke hukunci ba, sannan in ci gaba da rayuwa,” in ji shi.
Kyaftin ɗin na Portugal ya ce ita haka dama rayuwa take hatta ta ɗan ƙwallo, tana cike da nasara da rashin nasara.
“Wannan ita ce ƙwallon ƙafa, wannan kuma ita ce rayuwar ɗan ƙwallo. Wani lokaci ka yi nasara, wani lokaci kuma ka sha kaye, kuma dole ne ka ci gaba da rayuwa,” in ji shi.
Ronaldo, wanda shi ne kan gaba a jerin waɗanda suka fi zura ƙwallaye a tarihin ƙwallon ƙafar maza ta ƙasashe, ya ce zai bar Gasar Kofin Duniya cikin kwanciyar hankali.
“Gaskiyar magana ita ce babbar nasarar da na samu tare da ƙasar Portugal ita ce lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai a shekarar 2016. A gare ni, wannan nasara tana da muhimmanci kamar lashe Kofin Duniya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Saboda haka zan bar wannan gasa cikin kwanciyar hankali. Na yi iyakar ƙoƙarina, kuma rayuwa za ta ci gaba.”
Ronaldo ya lashe Gasar Kofin Nahiyar Turai tare da Portugal a shekarar 2016, amma bai taɓa lashe Gasar Kofin Duniya ba.
Mafi nisan da ya kai a gasar shi ne wasan kusa da na ƙarshe da Portugal ta buga shekaru 20 da suka gabata.