Babu dalilin kara wa’adin dokar ta-baci a jihohi uku —Karasuwa
Kwamishinan Ruwa na Jihar Yobe, Alhaji Yakubu Sidi Karasuwa ya bayyana idan har Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin dokar ta-baci a jihohin Yobe da Borno da Adamawa ta nuna da ma can akwai niyyyar hakan, saboda wasu boyayyun manufofinsu amma suka tsaya suna rara-gefe.Alhaji Yakubu Sidi Karasuwa da ake masa lakabi da ‘guguwar fasa lema’ […]
Kwamishinan Ruwa na Jihar Yobe, Alhaji Yakubu Sidi Karasuwa ya bayyana idan har Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin dokar ta-baci a jihohin Yobe da Borno da Adamawa ta nuna da ma can akwai niyyyar hakan, saboda wasu boyayyun manufofinsu amma suka tsaya suna rara-gefe.
Alhaji Yakubu Sidi Karasuwa da ake masa lakabi da ‘guguwar fasa lema’ ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya sakamakon kartar kasar da wasu ’yan adawar jihohin ke yi na sai a sake kara wa’adin dokar ta-baci a jihohin uku da Jam’iyyar APC ke mulkinsu.
Alhaji Yakubu Karasuwa ya kara da cewa wannan rashin zaman lafiya da ke faruwa a jihohin uku, musamman Yobe, ba kawai a jihohin aka fara samun irin wannan barazana ba domin a baya a yankin da Shugaban kasa ya fito wato Neja-Delta an yi fama da haka, amma ba a sa musu dokar ta-baci ba, sai ma nada kwamitin sasantawa da marigayi Shugban Umaru Musa ’Yar’aduwa ya yi.
A cewar kwamishinan, ba adalci ba ne a kara wa’adin dokar domin dokar da ake kokarin mayar da ita ga al’ummomin jihohin ba komai ba ce illa tauye hakkin al’ummomin saboda babu wani abin a zo a gani da dokar ta haifar illa sake dagula harkokon yau da kullum.
Don haka ya kirayi ’yan majalisar dokoki ta kasa su fitar da son rai su fada wa bangaren zartaswa da Shugaban kasa ke jagoranci gaskiyar lamari domin mayar da dokar ta-baci ga a jihohin tamkar biya wa wasu da ba sa kaunar ci gaban jihohin ne bukatunsu na kashin kai.