Babu dan majalisar da zai karbi miliyoyin Naira don yin ado – RMAFC

Shugaban Hukumar Tara kudin Shiga da Raba shi da kuma Tsara Albashi da Hakkokin Ma’aikata ta kasa (RMAFC) Elias Mbam ziyarci Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki don tantance masa alawus din kayan ado da kowane sanata da dan majalisar tarayya ya kamata ya samu bayan da wasu kafafen watsa labarai suka ce ’yan majalisun […]

Babu dan majalisar da zai karbi miliyoyin Naira don yin ado – RMAFC

Shugaban Hukumar Tara kudin Shiga da Raba shi da kuma Tsara Albashi da Hakkokin Ma’aikata ta kasa (RMAFC) Elias Mbam ziyarci Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki don tantance masa alawus din kayan ado da kowane sanata da dan majalisar tarayya ya kamata ya samu bayan da wasu kafafen watsa labarai suka ce ’yan majalisun biyu za su karbi miliyoyin Naira don sayen kayan adon.

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban Hukumar ta RMFAC Elias Mbam tare da jami’ansa suka ziyarci Sanata Saraki a ofishinsa domin yi masa bayani kan alawus din na kayan ado.
A wani sako da ya tura a shafinsa na Tweeter, Sanata Bukola Saraki, ya ce, Shugaban Hukumar RMAFC “ya zo ofishina don fayyace alawus din kayan adon, wanda Naira dubu 506 da 600 ne aka ware wa kowane sanata a shekara.”
Ya ce shugaban ya ziyarce shi ne saboda yunkurin da Hukumar RMAFC ke yin a rage albashi da alawus-alawus na ’yan majalisun biyu, inda ya ce, kayyade alawus-alawus na ’yan majalisun hakki ne na hukumar. Kuma Hukumar RMFAC za ta buga bayanan alawus-alawus din a shafinta na intanet. “ýYanzu aka shaida min Hukumar RMFAC za ta buga dalla-dallar bayanan alawus dina shafinsu na intanet. Sakamakon kalubalen da ke fuskantar kasar nan, Hukumar RMFAC za ta rika duba alawus din domin dacewa da hakikanin yadda tattalin arzikin kasa ke ciki.
A ranar Talata ne wasu kafafen watsa labarai suka bayar da rahoton cewa wakilan majalisun dattawa da ta wakilai za su samu Naira biliyan 8 da miliyan 640 a matsayin alawus din kayan ado.
Rahotannin sun ce za a biya kowane daga cikin sanatocin da ’yan majalisar wannan kudi ne kai-tsaye zuwa asusunsa na banki, kuma wannan kudi bai hada da alawus din kayan daki da na gida da na mota ba. Jaridar Thisday wadda ta fara buga labarin ta ce kowane dan Majalisar Wakilai daga cikin su 360 zai samu Naira miliyan 17 da rabi a shekara, yayin da kowane sanata daga cikin sanatoci 109 zai samu Naira miliyan 21 da rabi
Ta ce, alawus din kayan ado kamar alawus din kayan daki da na mota, zai kasance na shekara hudu a dunkule ga ’yan majalisar 469 gaba dayansu, yayin da za a rika biyansu alawus din gida shekara-shekara.
Jaridar ta ce, bisa amincewar Hukumar RMAFC, alawus din kudin gida ga masu rike da mukaman siyasa galibi kashi 200 na albashinsu na shekara, yayin da alawus din kayan daki yake kashi 300, sai bashin mota kashi 400 na albashinsu na shekara.
A cewarta, kowane sanata daga cikin sanatoci 107 baya ga shugaba da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa zai karbi Naira miliyan hudu da dubu 52 da 800 a matsayin alawus din gida, kuma za a rika biyansu wannan adadi ne duk shekara inda zai kama Naira jimilla Naira miliyan 433 da dubu 649 da 600, yayin da Gwamnatin Tarayya za ta samar da gida ga shugaba da mataimakin shugaban Majalisar Dattawan. Su kuma ’yan Majalisar Wakilai za su amshi Naira miliyan 3 da dubu 970 da 425 kowannensu a matsayin kudin gida da zarar sun kama aiki. Wannan yana nuna wakilai 358 ban da shugaba da mataimakin shugaban majalisar za su amshi jimillar Naira biliyan 1 da miliyan 421 da dubu 412 da 150 a matsayin alawus din gida, yayin da Gwamnatin Tarayya za ta samar da gida ga shugaba da mataimakinsa.
Rahoton dai ya fusata ’yan Najeriya inda suka rika amfani da shafukan zumunta na intanet suna caccakar ’yan majalisar dokokin.
’Yan Najeriya cikin fushi sun rika cewa wannan matakin babu adalci ganin galibin ’yan majalisar ba su kare ’yancin talakawa.
Wani mai suna Japeth Omojuwa, ya bayyana wadannan alawus-alawus a matsayin “hauka,” inda ya ce sun wuce gona da iri.Shi kuwa Elnathan John, ya bukaci ’yan majalisar ne kan su ji tsoron Allah ka da su karbi kudin saboda a cewarsa “Duk wanda ya karba ba zai iya kare kansa a gaban Ubangiji ba.”
Ita kuwa Fatima Askira cewa ta yi akwai tsofaffin gwamnoni a cikin ’yan majalisar kuma sun karbi makudan kudi a jihohinsu, ga shi kuma za su karbi wasu kudaden a majalisa.
Hatta a cikin wakilan majalisar dokokin wasu sun soki yawan alawus dain da aka ambata, inda Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma Dino Melaye ya ce “Bai kamata muna maganar canji mu karbi alawus din Naira biliyan tara ba. Sanata Dino Melaye ya bayyana wa gidan talabijin na AIT cewa biyan alawus din Naira biliyan tara ga ’yan majalisun biyu domin sayen tufafi bai dace ba, idan aka dubi matsanancin halin da kasar nan take ciki. Sanata Melaye, ya ce gwamnoni sun kasa biyan albashin ma’aikata, kuma fannoni da dama sun tabarbare a kasar nan, don haka ba ya goyon bayan biyan milyoyin Naira da suna alawus ga ’yan majalisa.
“Ina nan kan bukatata ta a rage albashin ’yan majalisar tarayya da na dattawa. Domin ba zai yiwu muna maganar canji kuma a ce a biya mu biliyoyin kudin nan ba, a yayin da talakawa suke fama da talauci da yunwa,” inji Sanata Melaye.
Rahotanni sun ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar RMAFC ta binciki batun tare da mika masa rahoto, bayan da wasu mukarrabansa suka ankarar da shi kan takaddamar da ake yi game da biyan wannan tsugugun kudi, jim kadan da dawowarsa daga Afirka ta Kudu.