Babu dan PDP daga Bauchi da zai yi biyayya ga Sheriff – Mai’auduga
daya daga manyan ’ya’yan Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi, kuma daraktan yakin neman zabe na tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Bala Abdullahi Mai’auduga ya ce babu dan PDP na gaskiya a jihar da zai yi biyayya ga shugabancin Ali Modu Sheriff da ya ce wasu tsirarin mutane tsirari suka […]
daya daga manyan ’ya’yan Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi, kuma daraktan yakin neman zabe na tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Bala Abdullahi Mai’auduga ya ce babu dan PDP na gaskiya a jihar da zai yi biyayya ga shugabancin Ali Modu Sheriff da ya ce wasu tsirarin mutane tsirari suka nada shi a matsayin sabon shugaban PDP na kasa.
Alhaji Bala Mai’auduga ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Bauchi, inda ya ce duk da dimbin mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana a Jam’iyyar PDP ke da su tun daga kananan hukumomi zuwa jihohi da tarayya babban abin mamaki shi ne a nada mutumin da ake zargin da alaka da batun Boko Haram.
Alhaji Bala Mai’auduga wanda ya ce ba su goyon bayan shugabancin Modu Sheriff ya bukaci sabon shugaban ya yi murabus a kashin kansa. “Babu wata jam’iyya da ta kai PDP yawan magoya baya a Nahiyar Afirka, tun bayan zaben 2015 na tsammaci cewa mun koyi wasu darussa a PDP. Ni ne babban daraktan yakin neman zaben tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a shiyyar Bauchi ta Kudu gaskiyar magana shi ne ba na goyon bayan Ali Modu,” inji Bala Mai’auduga.
Ya kara da cewa PDP ba shegiya ba ce tana da uba da uwa kuma wadanda suka nada Ali Modu kowa ya san cewa ba da su aka kafa jam’iyyar ba tun lokacin tana G34.
Ya ce matukar aka ci gaba da dauki-dora a PDP, zai yi matukar wahala ta sake kafa gwamnati a Najeriya domin yanzu kan mutane ya waye a siyasance. “Ya kamata a fahimci cewa siyasar dauki-dora ta wuce a Najeriya kuma duk lokacin da za a zabi mutum ko ba shi mukami a tabbatar cewa ba a zarginsa da wasu laifuffuka,” inji shi.
Ya ce “Muna kira da babbar murya ga Alhaji Ali Modu Sheriff ya fahimci cewa jihohi da dama ba sa goyon bayan shugabancinsa, don haka ya kamata ya jefar da kwallon mangoro ya huta da kuda.”