Babu dan takarar da za mu mara wa baya sai Buhari – dangwaggo
Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Buhari , kuma daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar nan a jam’iyar APC, ya ziyarci Sakkwato a Litinin da ta gabata cikin zagayen da yake yi na neman goyon bayan mambobin jam’iyar da aka amince su yi zaben fitar da gwani na jam’iyyar nan da mako mai zuwa. Tsohon […]
Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Buhari , kuma daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar nan a jam’iyar APC, ya ziyarci Sakkwato a Litinin da ta gabata cikin zagayen da yake yi na neman goyon bayan mambobin jam’iyar da aka amince su yi zaben fitar da gwani na jam’iyyar nan da mako mai zuwa.
Tsohon Shugaban wanda ya yi dogon bayani ga mahalarta taron, ya ce ‘Ina son ku sani zuwa yanzu ba wani abu da zan fadi wanda ban fade shi a baya ba, sai dai ana fadin waka a bakin mai ita tafi dadi, don haka zan taba wani abu da suka dame mu al’ummar Najeriya kuma suke damun kasar nan.
Akan wannan tsari na tafiyar jam’iya da aka sanya zaben fitar da gwani domin ya fuskanci shugaban kasa mai ci a zaben badi, aka zakulo mutane masu hazaka irinku, don ku wakilci sauran mambobin jam’iya kan fitar da gwaninku a dukkan jihohin kasar nan, to yanzu kwana tara ya rage ku yi zabin, abin da nake fata shi ne ku yi tuna baya daga 1999 lokacin da PDP ta kama mulkin kasar nan tarayya da jihohi 24 daga cikin 36 na kasar nan, a lokacin nan kun sani muna da kamfanin jiragen sama da na ruwa, jirgin kasa yana yi, ita kanta wutar lantarki kusan karfin wutar a wancan lokacin da yanzu ddaya ne, amma bambancin shi ne an ce an kashe biliyan biliyan 20 kan wuta kawai babu wutar, ba kudin. ‘Yan majalisar tarayya sun damu da cece kucen da ‘yan Najeriya ke yi kan cin hanci da rashawa na abu uku, waton ita kanta wuta da kudin sallamar ma’aikata(fensho) da sha’anin kudin man fetur, suka yi terere don jin ra’ayin jama’a a Abuja da sauran jihohi, da suka gama aikin suka tura fadar shugaban kasa don gyara lamurran har yanzu shiru kamar an shuka dusa.’ A cewarsa.
Buhari ya ce ‘Sa’annan abin da ya shafi rikicin kasar nan na Arewa maso gGabas sai ga shi sojojin kasar nan na aikata abin da ba a saba gani ba, na ba jaridun kasar waje da gidajen rediyonsu labarin irin musibar da suke ciki, ana tura su, su je su yi fada babu makamai, balle harsashi kuma shugabanninsu sun gudu, sun barsu, ‘yan majalisa suka waiwayi maganar ita ma aka kasheta.
Ku mahalarta taron da wadanda ke gida ina son ku yi tunanin kananan hukumominku a 1999 zuwa yau, mene ne matsayin makarantu da asibitoci da hanyoyi da kudin da ake samu, wannan ne zai tabbatar wa mai tunani duk ya bari PDP ta sake wata sukuwa ta shekara hudu, to daga badi kila ba za mu iya gane junanmu ba, duk wadannan kalaman nawa babu sharri ko yarfe a ciki gaskiya nake fadi, kuma mun san sha’anin mulki in ba gaskiya bai dorewa. Tun da PDP ba ta da niyar adalci, ya kamata mu cire ta, ta hanyar da kundin tsarin kasa ya yarda da shi, wannan kuma ba zai samu ba sai an hada kai, bai kamata saboda wani bambanci da ke tsakaninmu ba mu kasa hada kai don ceto kasar nan daga hannun azzalummai.’in ji shi.
‘Da wannan nan nake yi wa matasa gori, saboda mutane da yawa suna fadar in barwa matasa mulki don na tsufa. Matasa masu zuwa wurina kan siyasa ina fada musu a lokacin da nake da shekarunsu duk abin da dan siyasa ke nema a kasar nan Allah ya yi min sha’anin kaddara ne kawai don a inda na yi gwamna yanzu jiha shida ne, na yi ministan mai shekara uku da wata uku, na yi shugaban kasa wata 20; na jagorancin PTF sai da muka kai asusun ajiyarmu na da biliyan 53, Allah ya rufa asiri ba mu zalunci kowa ba, duk da binciken da aka yi. Don haka ina gaya wa yaran nan ba wani abu nake samu ba, wannan abin da muke yi taya su ne muke yi duk son mulki na don da alamu ban fiye son kudi ba, ina kira da su zo mu hada karfe da karfi, mu kawar da PDP don kawar da halin matsi da muke ciki.
A wurin taron da aka gudanar a dakin taro na gidan saukar shugaban kasa na jiha, shugaban kkungiyar shugabannin jam’iyyar na Jihar Sakkwato, Alhaji Muhammad Dangwaggo ya yi magana a madadin sauran
‘Duk dan Arewa yana bakin cikin abin da ke faruwa a yankinsa Allah ya ba ka kasar nan ka gyara mana ita, Mai girma ina son in ba ka hakuri na gaya wa mu Sakkwato mun yi matsaya muna da dan takararmu, shi ne Buhari, ba mu da wani dan takara da za mu mara wa baya in ba Buhari ba.’ a cewar dangwaggo.