Babu dangantaka tsakanina da Tiwa Sabage – Lola Sabage
Tun lokacin da mawakiya Lola Sabage ta fara waka a shekarar 2013 ne masoya wakoki suka rika cewa tana da dangantaka ta jini da fitacciyar mawakiya Tiwa Sabage. Masu magana sun ce komai nisan jifa to kasa zai fado, domin cikin wata hira da mawakiyar ta yi ’yan jarida a Legas ta bayyana babu dangantaka […]
Tun lokacin da mawakiya Lola Sabage ta fara waka a shekarar 2013 ne masoya wakoki suka rika cewa tana da dangantaka ta jini da fitacciyar mawakiya Tiwa Sabage. Masu magana sun ce komai nisan jifa to kasa zai fado, domin cikin wata hira da mawakiyar ta yi ’yan jarida a Legas ta bayyana babu dangantaka tsakaninta da Tiwa Sabage.
Ta ce: “Babu wani abu da ya hada mu face sunan mahaifi iri daya (Sabage). Ita fitaccciyar mawakiya ce a Najeriya. Ina girmamata. Amma sunana Lola Sabage, ina da salo da tsarina, ina kuma so in yi abin da nake ganin shi ne mafi dacewa da ni. Na zo kasar nan ne don in nuna wa ’yan Najeriya fasahar da nake ita, ba kuma na zo don in kwaikwayi Tiwa ba ne. Babu wata dangantaka ta jini tsakanina da ita.
Mawakiyar ta ce ba wai ta zo Najeriya don ta yi gasa da Tiwa Sabage ba ne, “Ina girmama ta, ina kuma yaba wa abubuwan da take yi, zan nuna wa mutane ba gaba ko gasa na zo in yi da ita ba. Za mu yi waka tare kamar yadda ’yan uwan juna Tuface da kanensa Joel suka yi. Matsalata da ’yan Najeriya ita ce komai sai an yi masa wata fassara. Ba kuma zan yi waka da ita ba ne don ta fito da ni.”
Ta ce babban burinta ta kasance daya daga cikin mawakan da za su kafa tarihi a duniyar mawaka.