‘Babu diyyar da za a biya ’yan Najeriya da suka bar kadarori a Afirka ta Kudu’
An shawarci waɗanda suka mallaki kadarori bisa doka da su sayar da su maimakon jiran gwamnati ta biya su diyya.
Ministar da ke kula da harkokin Fadar Shugaban Ƙasa ta Afirka ta Kudu, Khumbudzo Ntshavheni
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce ba za ta biya diyyar ’yan Najeriya da sauran baƙin da suka bar kadarorinsu bayan an kwashe su daga ƙasar ba.
Ta bayyana cewa kadarorin da aka mallaka ba bisa ƙa’ida ba ko kuma waɗanda ke wuraren da hukumomi ba su amince da su ba ba su cancanci biyan kowace irin diyya ba.
- Harin Rasha ya yi sanadin mutuwar dalibar Najeriya a Ukraine
- Matashi ya kashe abokinsa da adda a Kuros Riba
Ministar da ke kula da harkokin Fadar Shugaban Ƙasa ta Afirka ta Kudu, Khumbudzo Ntshavheni, ta sake jaddada wannan matsayi, inda ta yi watsi da batun cewa gwamnatin Pretoria za ta biya ’yan Najeriya diyya.
Kalaman nata sun biyo bayan bayanin muƙaddashin Babban Kwamishinan Najeriya a Afirka ta Kudu, Temitope Ajayi, wanda ya ce gwamnatin Najeriya na nazarin hanyoyin da za a bi domin neman diyyar ’yan ƙasar da suka rasa ko suka bar kadarorinsu bayan ficewarsu daga Afirka ta Kudu.
Da take mayar da martani, Ntshavheni ta ce gwamnatin Afirka ta Kudu ba za ta ɗauki alhakin biyan diyya kan kadarorin da aka bari ba.
Ta shawarci waɗanda suka mallaki kadarori bisa doka da su sayar da su ta hanyar kasuwar kadarori ta Afirka ta Kudu maimakon jiran gwamnati ta biya su diyya.
“Mutanen da ke da kadarorin da aka mallaka bisa doka su sayar da su a kasuwar kadarori,” in ji ta, tana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta ɗauki alhakin kadarorin da aka yi watsi da su ba.
A makonnin baya-bayan nan, dubban baƙi, ciki har da ’yan Najeriya, sun bar Afirka ta Kudu bayan zanga-zangar ƙyamar baƙi da kuma wa’adin da wasu ƙungiyoyi suka bayar ga baƙin da ke zaune ba bisa ƙa’ida ba su fice kafin ranar 30 ga Yuni.
Haka kuma, ƙasashe da dama sun kwashe wasu daga cikin ’yan ƙasashensu daga Afirka ta Kudu sakamakon tashin hankalin.