Babu gawar mutumin da aka tsinta a gefen hanya a Kano — ’Yan sanda

Hasalima shi ya ɗaure kansa da kebur ya kwanta a gefen hanya.

Babu gawar mutumin da aka tsinta a gefen hanya a Kano — ’Yan sanda

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce mutumin da aka yayata cewar an tsinci gawarsa a kan titin zuwa Gidan Gwamnatin Kano na nan da ransa.

Kakakin Rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan, yana mai cewa mutumin da hannunsa ya ɗaura wa kansa igiyar da aka gani a wuyansa ake kuma zargin da ita aka kashe shi.

Idan za a iya tunawa dai, a jiya ne aka wayi gari da ganin mutumin yashe a kan titin zuwa Gidan Gwamnatin Kano da igiya ta shaƙe wuyansa, dalilin da aka yi zargin ɓata-gari ne suka halaka shi.

Sai dai a safiyar ranar Talata ne kakakin rundunar ’yan sandan Kano ya musanta hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce yanzu haka mutumin na hannunsu har zuwa lokacin da za su kammala bincike.

“Bayan mun kai shi asibiti ya faɗi gaskiya. Ba abin da aka kwata a wajensa. Hasalima shi ya sawa kansa kebir ya kwanta a wajen. Yanzu haka yana hannun ’yan sanda,” in ji Kiyawa.