Babu Gwamnan da aka fi bincika a tarihin Najeriya sama da ni – Tinubu
Tinubu ya ce duk da binciken na kwa-kwaf da aka yi masa babu abin da aka samu
Asiwaju Bola Tinubu
Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce babu wani Gwamna a tarihin Najeirya da ya fuskanci bincike kamar shi.
Ya ce duk da binciken na kwa-kwaf da aka yi masa babu abin da aka samu.
- DAGA LARABA: Jabun Kayayyaki: Ina Hukumar SON Ta Shiga Ne?
- ’Yan bindiga sun sace wasu mata a kantin magani
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata a tattaunawarsu da kafar BBC yayin ziyarar da ya kai London.
Dan takarar ya kuma bayyana ce-ce-ku-cen da ake yi game da dukiyarsa a matsayin hassada da kyashi.
Tinubu ya kuma ce a duk cikin ‘yan takarar Shugaban Kasa shi ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya a zaben 2023 mai zuwa.
Ya kara da cewa, yana da yakinin muddin aka gudanar da sahihin zabe a 2023, shi ne zai lashe shi.
Tsohon Gwamnan ya ce, fannin tsaro da tattalin arziki su ne fannonin da zai bai wa muhimmanci muddin aka zabe shi Shugaban Kasa.