Babu hannun Gwamnatin Tarayya a harin da a kai wa Buhari – Sufeto Janar
Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Malam Suleiman Abba ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta da hannu a harin bam da aka kai don halaka tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, kamar yadda rahoton farko na binciken ‘’yan sanda ya gano.Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Malam Suleiman Abba yana bayyana haka […]
Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Malam Suleiman Abba ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta da hannu a harin bam da aka kai don halaka tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, kamar yadda rahoton farko na binciken ‘’yan sanda ya gano.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Malam Suleiman Abba yana bayyana haka a ranar Litinin bayan ya gana cikin sirri da manyan jami’an ’yan sanda domin tsara dabarun yadda za a fuskanci kalubalen tsaro da kasar nan ke fama da shi.
Ya ce rahoton farko na binciken da ’yan sanda suka gudanar ne ya gano haka.
Janar Buhari, wanda shi ne jagoran babbar jam’iyyar adawa ta APC, ya tsallake rijiya da baya a harin bam da aka kai masa a ranar 23 ga Yuli a Kaduna, harin da aka hakikance an yi nufin hallaka shi ne.
“Harin bam din ya rutsa da ni yau a kan titin Ali Akilu da ke Kawo Kaduna da misalin karfe 2:30 na rana a kan hanyata ta zuwa Daura,” inji Buhari bayan kai harin.
Ya kara da cewa, “Abin takaicin a filin yake yunkurin kashe ni ne, an zo da wata mota da mugun gudu da ta rika kokarin shan gaban motar jami’an tsarina, amma motar jami’an tsarina ta hana ta wucewa. Muna isa kusa da kasuwar Kawo ne suka yin amfani da damar tsagaitawarmu suka yi yunkurin kara wa motata kuma nan take suka tayar da bam wanda ya lalata dukkan motoci uku na tawagarmu.”
Babu wata kungiya da ta yi da’awar daukar nauyin kai harin, a daidai lokacin da ake zargin Gwamnatin Tarayya da kai harin, kuma tun lokacin ’yan sanda suka fara bincike.
Abba ya ce, “Tsohon Sufeto Janar ya kafa kwamitin bincike na kwararru domin gudanar da ingantaccen bincike.” Kuma a cewarsa, kwamitin wanda ya kunshi kwararrun masana kwayar halittar mutum sun ziyarci wurin da bam din ya tashi da wadanda harin ya shafa a asibiti kuma ya gana da Buhari da wadanda suke tare da shi.
“Zuwa yanzu sun fitar da sakamako, kuma sakamakon binciken shi ne babu hannun Gwamnatin Tarayya a ciki,” inji Shugaban ’Yan sandan.
Malam Abba ya ce mutum guda da aka kama bisa zargi kan lamarin sojoji na rike da shi. Kuma ba zai iya cewa ko wanda ake zargin ya yi wani bayani mai amfani ba.
Ya kuma ce, ’yan sanda sun kama wanda ake zargi a lokuta biyu ko uku a baya kan alaka da wani laifi amma ba za su fada ba.
A ranar 23 ga Yuli ne wasu tagwayen bama-bamai suka tashi a Kaduna inda aka nufi Buhari da kuma fitaccen malamin addinin Musulunci nan Sheikh dahiru Bauchi, kuma sama da mutum 80 ne suka rasu a hare-haren biyu.