Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu
Mai Shari’a Ejiro Kubenje ya ce babu wata ayar tambaya kan mutanen biyu game da rasuwar Mohbad.

Kotun Majistire da ke zama a Sabo a unguwar Yaba ta Jihar Legas ta wanke mawaƙi Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley da abokin aikinsa Samson Balogun Eletu, wato Sam Larry daga zargin hannu a mutuwar mawaƙi Aloba Oladimeji IleriOluwa, wanda aka fi sani da Mohbad.
Mai Shari’a Ejiro Kubenje, wanda ya karanta hukuncin ya ce babu wata ayar tambaya kan mutanen biyu game da rasuwar Mohbad.
- Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS
- An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo
Haka nan ma kotun ta sallami Oodunni Ibrahim, wanda ake kira Primeboy da tsohon manajan Mohbad, Opere Babatunde.
Sai dai hukuncin ya ce za a gurfanar da ma’aikaciyar jinyar da ta kula da Mohbad gabanin mutuwarsa, wato Feyisayo Ogedengbe, da ɗaya daga cikin abokan marigayin, Ayobami Sadiq bisa tuhumar su da sakaci, wanda ya kai ga mutuwar matashin mawaƙin.
Ana iya tuna cewa, mutuwar Mohbad a shekarar 2023 dai ta janyo ce-ce-ku-ce matuƙa musamman a kafafen sada zumunta na zamani a ciki da wajen Nijeriya.
Kazalika, a wancan lokacin an gudanar da zanga-zanga a jihohin Legas da Oyo da Delta, don neman a binciki musabbabin mutuwar ta shi.