Babu ingantaccen tsaro a Mubi – ’Yan gudun hijira

Shugaban ’yan gudun hijirar Mubi da ke Yola, Malam Sa’ad Bello ya ce Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ba ta tabbatar da ingantaccen tsaro a Mubi da wasu wurarrn da sojojib suka karbe iko da su daga hannun Boko Haram ba. Malam Sa’ad Bello ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da […]

Babu ingantaccen tsaro a Mubi – ’Yan gudun hijira
Babu ingantaccen tsaro a Mubi – ’Yan gudun hijira

Shugaban ’yan gudun hijirar Mubi da ke Yola, Malam Sa’ad Bello ya ce Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ba ta tabbatar da ingantaccen tsaro a Mubi da wasu wurarrn da sojojib suka karbe iko da su daga hannun Boko Haram ba.

Malam Sa’ad Bello ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Yola, inda ya ce “sakamakon rayuka da dukiya da aka rasa a hare-haren da aka kai yankunan za a dauki lokaci mai tsawo kafin al’amura su koma daidai a garuruwan da harin ya shafa.”
Ya ce sun yaba wa sojoji amma ya kamata a tabbatar da cewa wadanda aka biya musu kudin mota suka koma gidajensu sun samu isasshiyar kariya da tsaro daga sake kai musu hari da kuma magance illar da za su iya haduwa da ita daga shakar warin gawarwaki a garin.
Malam Sa’ad ya ce “Kodayake sojoji ne kawai za su iya tabbatar da tsaro a wuraren suke a yanzu. Mu kuma mu ba da shawarwari game da lafiyar jiki domin mun kasance masu aiki da likitoci ko kuma kungiyar agaji ta Red Cross.”
Ya bukaci mutanen da ke son komawa gidajensu cewa su tabbatar da tsaron wajen kuma su je a duba lafiyansu kafin su koma.
Ya ce “Hukumar NEMA da takwararta ta Jihar Adamawa (SEMA) sun binne gawarwakin da suke wari a garin Mubi da ke sanya wari a garin. Amma har yanzu muna kyautata zaton za a samu gawarwaki a daji da wasu gidajen. Muna iya kokarinmu da mu ga cewa an samu kyakkyawan tsaro domin kare lafiyar jama’a.”
Ya ce a cikin yara 128 da suka samu a wajen tsaronsu, guda 7 ne kawai suka hadu da iyayensu.