Babu ja da baya a yunkurin ceto al’ummar Jihar Zamfara – Ibrahim Gusau
A yayin da guguwar siyasa ke kadawa a kasar nan, daya daga cikin masu neman tsayawa takarar Gwamnnan Jihar Zamfara a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Ibrahim Shehu Gusau, ya ce ba zai ja da baya ba wajen ganin ya ceto al’umar jihar daga abin da ya kira mawuyacin halin da suke ciki. Alhaji Ibrahim Shehu […]
A yayin da guguwar siyasa ke kadawa a kasar nan, daya daga cikin masu neman tsayawa takarar Gwamnnan Jihar Zamfara a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Ibrahim Shehu Gusau, ya ce ba zai ja da baya ba wajen ganin ya ceto al’umar jihar daga abin da ya kira mawuyacin halin da suke ciki.
Alhaji Ibrahim Shehu Gusau ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana niyyarsa ta neman tsayawa takarar Gwamnnan Jihar a zaben 2015.
Alhaji Ibrahim Shehu ya ce ba za su ja da baya ko su yi nauyin jiki wajen shirin kwace mulki daga Jam’iyyar APC da Gwamna Abdul’Azeez Yari Abubakar ke shugabanta, domin ceto al’ummar Zamfara daga mulkin kama-karya da rashin alkibla da ake yi musu.
Ya nuna takaicinsa ka yanayin da jihar ta shiga a tsawon mulkin Jam’iyyar ANPP zuwa na
APC abin da ya ce ya janyo matsaloli masu yawa.
Mai neman takarar ya ce kadan daga cikin matsalolin da jihar ta fada sun hada da rashin ci gaba da mayar da jihar saniyar ware a cikin kasa.
Ya jinjina wa dattawa da matasan Jihar Zamfara kan hakuri da diyauchin da suka nuna ga
tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jihar duk da kangin wahala da rashin ingancin shugabanci da ake fuskanta a jihar.
Ya yi alkawarin idan ya samu zama Gwamnan Jihar zai fi mayar da hankali kan bunkasa ilimi da noma da samar da aikin yi da tsaro, kafin daukar wasu fannoni.
Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Sanata Hassan Mohammed Nasiha ya yi tsokaci ne kan sakacin gwamnatin jihar a karkashin Jam’iyyar APC wajen tsare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma rashin wasu tsare-tsare na ciyar da al’ummar gaba. Ya ce an samu karuwar talauci da jahilci a jihar fiye da sauran lokuta.
Sai ya yaba kokarin Injinya Ibrahim Shehu Gusau na hada kan jama’a da kuma taimaka wa Jam’iyyar PDP da sauran al’ummar jihar, musamman tallafa wa dalibai da marasa galihu da
samar da guraben aikin yi ga ’yan asalin jihar a Gwamnatin Tarayya.
Taron ya samu halartar manyan baki ciki har da ’yan Majalisar Wakilai 12 da Sanatoci biyar da shugabanin Jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara.