Babu ja da baya game da batun – Gwamna El-Rufa’i
Shi kansa Gwamna El-Rufa’i bayyana cewa ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati da masu hannu da shuni da ke abokantaka da jami’an gwamnati ne wadanda ake bai wa irin wadannan kujeru, duk kuwa da cewa suna da kudin da za su biya wa kansu da iyalansu.Ga dukkan alamu El-Rufa’i ba ya da niyya yin sassauci […]
Shi kansa Gwamna El-Rufa’i bayyana cewa ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati da masu hannu da shuni da ke abokantaka da jami’an gwamnati ne wadanda ake bai wa irin wadannan kujeru, duk kuwa da cewa suna da kudin da za su biya wa kansu da iyalansu.
Ga dukkan alamu El-Rufa’i ba ya da niyya yin sassauci kan wannan matsayin day a dauka, domin kuwa ya sake jaddada matsayin nasa a lokacin da yake ganawa da al’ummar Zariya a farkon makon nan, inda ya ce ba zai canza ra’ayinsa ba.” Matakin da muka dauka ya janyo surutai, mun kuma ce ba za mu dauki kudin gwamnati mu biya wa wadansu zuwa aikin hajji ba, muna kuma kara sanar da jama’a cewa ba za mu janza ra’ayinmu ba, domin shi aikin hajji yana cikin shika- shikan musulunci amma sai ga mai iko ko hali aka ce ya je. Ba a kuma ce a dauki kudin mutane a biya wa wadansu zuwa aikin hajji ba. Mun duba mun ga cewa kudin da ake biya wa manyan mutane zuwa hajji ya yi yawan da mu ba za mu iya ba. Mun gwammace mu yi amfani da wannan kudin wajen gyara makarantu da Asibitoci da gyara hanyoyi,” inji shi.