Babu ja da baya kan sake fasalin tattalin arzikin Najeriya — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta sauya fasalin ɓangaren tattalin arzikin Najeriya, tare da cewa wannan shirin shakka babu zai amfani ɗaukacin Afirka. Shugaban wanda ya yaba da alaƙar Najeriya da Faransa, ya shaida wa shugaba Emmanuel Macron cewa babu gudu ba ja da baya kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara yi. […]

Babu ja da baya kan sake fasalin tattalin arzikin Najeriya — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta sauya fasalin ɓangaren tattalin arzikin Najeriya, tare da cewa wannan shirin shakka babu zai amfani ɗaukacin Afirka.

Shugaban wanda ya yaba da alaƙar Najeriya da Faransa, ya shaida wa shugaba Emmanuel Macron cewa babu gudu ba ja da baya kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara yi.

Da yake jawabi a wajen liyafar cin abincin dare da gwamnatin Faransa ta shirya masa a Palais des Elysée da ke birnin Paris a daren Alhamis, Tinubu ya ƙarfafa gwiwar ‘yan Najeriya da Faransa da su ci gaba da ƙulla kyakkyawar alaƙar da ƙasashen ke yi.

Tinubu ya ce Afirka ba ta da wani zaɓi illa gina nahiyar da za ta bunƙasa fannoni da dama da suka kamata, da kuma inganta shirin walwalar jama’arta, yana mai nanata cewa gwamnatocin nahiyar sun himmatu matuƙa wajen inganta rayuwar al’umma.

A nasa jawabin, Shugaba Macron ya yaba da shugabancin Najeriya a nahiyar Afirka, musamman dangane da rawar da take takawa a matsayin ‘babbar yaya’ ga nahiyar.

Ya kuma yaba wa ‘yan Najeriya bisa ƙwazo da basirar da suke da ita, yana mai ambato sunayen Farfesa Wole Soyinka da ya taɓa lashe kyautar Nobel da mawaƙi Femi Kuti a matsayin waɗanda suka yi fice a duniya.

“Najeriya ta samu ’yanci ta hanyar karɓe mulki da sojoji sannan Shugaba Tinubu wanda ya kawo sauyi a fannin tattalin arziki a Legas, yanzu ya ɗauki hanyar kawo sauyi a ƙasar baki ɗaya,” inji Macron.