‘Babu jami’in jakadancin da zai bar Sudan sai an kwashe duk ’yan Najeriya’
Babu jami’in ofishin jakadancin da zai fice daga Sudan har sai an kwashe duka ’yan kasar.
Jakadan Najeriya a Sudan, Ambasada Safiu Olaniyan ya yi karin haske game da halin da ’yan kasar nan suke ciki wadanda suka makale a kasar da rikici ya kazanta.
Ya bayyana cewa ofishin Jakadancin Najeriya da ke Sudan din na jiran sahalewar gwamnatin kasar Masar da ta Najeriya kafin wucewar manyan motocin da suka kwashe ’yan kasar daga Sudan, ta kan iyakar kasar Masar din.
- City ta karbe ragamar teburin Firimiyar Ingila daga hannun Arsenal
- Mutum miliyan 4.3 za su fuskanci matsananciyar yunwa a jihohi 3 na Najeriya —MDD
A wani sakon murya da ya aike wa hukumar da ke kula da ’yan Najeriya mazauna kasashen waje, Mista Olaniyan ya ce abin da ake bukata ga wadanda ke kan iyakar Sudan da Masar shi ne sahalewar hukumomi, kuma duk abin da ya kamata a yi game da hakan an yi shi.
Ya kara da cewa ba ofishin jakandancin ba ne ke da alhakin samar da motocin.
Ya ce ofishin na bin umarnin Ma’aikatar Jin-kai da ta bayar da Agajin Gaggawa NEMA.
Jakadan Najeriyar ya kuma tabbatar wa iyaye da dalibai cewa jami’an ofishin jakandancin a birnin na Khartoum suna tare da ’yan kasar a cikin wannan mawuyacin hali na yaki da ake ciki.
Mista Olaniyan ya kuma yi kira ga wadanda za a kwason da su guji far wa jami’an ofishin jakadancin a matsayin wani martani na huce takaici.
Sabanin yadda tun da farko aka yada jita-jita, ya bayyana cewa babu jami’in ofishin jakadancin da zai fice daga Sudan har sai an tabbatar da kwashe duka ’yan kasar.