Babu jarin da makaho zai samu kamar ilimi – Ibrahim Inuwa
Mene ne takaitacen tarihinka? Sunana Ibrahim Inuwa an haife ni ne a 1972 a nan garin Bauchi, na yimakarantar firamare kamar sauran yara, inda wannan waki’a ta kwakule min ido ta same bayan na kammala firamare a makarantar firamare ta Shekal da ke garin Bauchi. Sai dai duk da matsalar da na samu maimakon ta […]

Mene ne takaitacen tarihinka?
Sunana Ibrahim Inuwa an haife ni ne a 1972 a nan garin Bauchi, na yimakarantar firamare kamar sauran yara, inda wannan waki’a ta kwakule min ido ta same bayan na kammala firamare a makarantar firamare ta Shekal da ke garin Bauchi.
Sai dai duk da matsalar da na samu maimakon ta kashe min kwarin gwiwa sai na kara dagewa na shiga Makarantar Horar da Makafi ta Bauchi lokacin tana Unguwar Jahun kafin a maida ta inda take yanzu a Unugwar Yelwa. A makarantar na fara karatu tun daga firamare saboda ilimin na musamman ne, dole na faro daga yadda makafi ke koyon haruffa har na nakalta, na kammala, ka ga na yi firamare sau biyu ke nan, ga ta Shekal ga ta Makafi, daga nan na shiga wata makaranta mai zaman kanta da wadansu Turawan Mishan daga kasar Ingila suka kafa a Jos da ke Jihar Filato, a nan na yi sakandare aji hudu, inda saboda matsalar rashin kudi iyayena suka dawo da ni Bauchi inda na yi firamaren makafi wadda akwai sakandare a cikinta, na kammala karatun sakandarena. Duk da cewa ina son in ci gaba da karatu a lokacin matsalar rashin kudin nan ta yi mini tarnaki sai a shekarar 2000 wato shekara bakwai baya aka dauke ni a Jami’ar Jos na yi karatun diploma kan ilimin nakasassu, daga nan na samu aiki a sashin kula da jin dadi da walwalar jama’a na karamar Hukumar Bauchi. A shekarar 2006 ne kuma na tafi Jami’ar Bayero da ke Kano inda na yi karatun digiri kan ilimi na musamman, da na dawo na ci gaba da aiki da karamar Hukumar Bauchi. Na yi aure ina da mace daya da ’ya’ya bakwai.
Wane aiki kake yi a karamar hukumar?
Ni ne jami’in da ke kula da jin dadin nakasassu, ka san aikin sashin kula da walwala da jin dadin Jama’a suna tafiya ne kafada-da-kafada da ilimi na musamman. A karkashin wannan sashi akwai sashin kula da makafi da sashin kulawa da nakasassu, da na kula da yaran da iyayensu suka haife su suka jefar da yara marasa galihu. Kuma aikina shi ne in tabbatar da cewa nakasassu sun samu shiga cikin al’umma cikin martabarsu da darajarsu na ’yan Adam su ma su yi rayuwa mai dadi. Shi ya sa aka saka ni nake kulawa da jin dadi da walwalarsu har na kai mukamin Maitaimakin Jami’in Kula da Jin Dadin Jama’a.
An dauki shekaru da wannan kaki’a ta kwakule maka ido ko za ka iya tuna yadda lamarin ya faru?
Kamar yanzu kuwa, ka san ba zan taba mancewa ba, akwai wani mutum ne da yake zaune a gidanmu sai ya bukaci in raka shi cikin daji mu je mu dawo, sai na bi shi muka tafi. Da muke je cikin daji sai ya kada ni ya danne ni ya daure hannuwana ya kuma sa wuka mai kaifin gaske ya kwakule mini idanuwana da karfi. Ya gudu ya bar ni cikin jini ga zatonsa na mutu, amma Allah da ikonSa Ya nufa da sauran shan ruwana a gaba, na rayu lokacin ina yaro karami. Amma na san lokacin mulkin soji ne, lokacin Gwamnan Jihar Bauchi Kanar Chris Abutu Garuba, wannan lamari ya girgiza al’ummar Jihar Bauchi a lokacin da gwamnatin kanta har gwamnati ta dauki nauyin jinyata. Sai dai abin bakin ciki a lamarin gwamnati idan wata gwamnati na aikin alheri in ba sa’a aka yi ba in wata gwamnati ta zo sai ta daina. Domin kafin na kammala makarantar sakandare sai na rasa tallafin da nake samu na karatu daga gwamnatin jihar hakan ya sa na wahala kwarai kafin na samu hanyar da na yi karatun diploma, shi ma karatun digiri din da na yi na wahala kwarai, koda yake na samu tallafin karatu (Scholarship), amma shi ma kudin ba ya zuwa a kan kari sai ka ga in bana ka samu, badi ba za ka samu ba, da haka har Allah Ya sa na kammala karatun. Kuma bayan rasa idanu biyu da aka kwakule na sake samun wata jararrabawa daga Allah inda na fadi na karye a hannuna ba ni da kudin yin jinya asibiti, sai aka yi mini dorin gida ba a dora kashin yadda ya kamata ba, amma Allah Ya ba ni lafiya hannun ya warke sai dai ka ga kamar lilo yakeyi ya gajarce. Alhamdulillahi na gode wa Allah saboda ina iyayin abubuwa da dama da hannun ciki har da amfani da na’urar kwamfuta, domin har na samu takardar shaidar iya kwamfuta daga cibiyar horar da ilimin kwamfuta ta Farfesa Iya Abubakar da ke Bauchi. Kuma bayan wadannan ina karantar da ilimin makafi don na koyar a lokacin da nake aikin koyon aikin malanta an tura ni makarantar sakandare na karantar.
Da yake kana aikin kyautata rayuwar makafi, a ganinka ta yaya gwamnati za ta taimaka musu?
A ganina ilimi shi ne babban jarin da za ka bai wa makaho da kowane nakasasshe har ya iya tsayawa da kafafunsa ya dogara da kansa. Wannan shi ne abin da ya fi kamata gwamnati ta maida hankali a kai. Mutanen da Allah ya jarrabe su irina kuma kada su karaya, saboda nakasa ba ita ce karshen rayuwa ba, sai mu rungumi kaddarar da Allah Ya jarrabe mu da ita na makanta mutum ya yi tunanin yadda rayuwarsa za ta ci gaba, idan kuwa mutum ya kashe zuciyarsa ya kasa yin komai saboda ya makance wannan shi ne farkon asarar rayuwarsa. Ya kamata ne tunda ka makance ka mike ka yarda da ikon Allah ka nemi taimakonSa ka yi karatu har Allah Ya sa ka tsaya a kan kafafunka ka ci gaba da rayuwa kai ma. Amma yaushe za ka yi ta jira kana tunani ka kasa aikata komai ka kasa tabuka komai kana jirar wani ya yi maka in bai yi maka ba fa? Saboda haka don ka makance dole ka ci gaba da rayuwa tunda ba ka mutu ba, ka dage mai ganin ma in bai dage ba rayuwar ba za ta tafi yadda ake so ba.
Shekarun baya kun kafa wata kungiya don kula da makafi ina aka kwana kan ayyukan kungiyar a Jihar Bauchi?
Eh, haka ne amma lokacin muna dalibai ne. Amma a gwamnatin da ta shude mun zauna da wani kwamishina a wancan lokacin mai suna Kyaftin Bala Jibrin mun dauko tsarin yadda za a taimake mu domin makafi su samu tallafin da za su yi karatu, sai kuma aka sauya masa ma’aikata, sai ya yi kokarin hada mu da jami’an gwamnatin da suka dace domin a tallafa wa nakasassun yadda za su samu ilimi mai inganci. Amma ka san sha’anin ba kowa ne ke da sha’awa da azama irin nasa na tallafawa makafin ba, ba mu samu nasarar wannan yunkuri na mai da makafi makaranta ba. Ka san sha’anin yau mafi yawancin ’yan Najeriya, talakawa da attajirai ba dukansu ne ke ganin martabar nakasasshe ba, muna shan wahala fiye da talakan da ba ya da nakasa saboda bukatu irin namu da muke da su na musamman. Ana ture mu ana mai da mu baya a kan abubuwa da dama, saboda larurar da muke da ita ba za mu iya yin gwagwarmaya domin ganin ana damawa da mu cikin kowane lamari ba. Amma na tabbata idan muka samu ilimi zai bambanta rayuwarmu da ta marasa ilimi kuma zai sa a yi da mu don rayuwarmu za ta inganta kwarai da gaske, shi ya sa muka yi wancan yunkuri.
A karshe mece ce fatarka?
Ba ni da wani buri face in samu dukan irin nasarorin da dan Adam ke samu a fagen ilimi. Ka ga a yanzu haka ina so in je in yi karatun digiri na biyu da na uku har in kai matuka a fannin da na kware, amma saboda rashin kudi abin zai yi mini wahala, wannan ne burin da nake da shi kuma har zuwa yau ban cika shi ba.