Babu jihar Arewa da ke da ƙwararrun malamai kaso 50 – Babangida Aliyu

Tsohon Gwamnan ya kuma ce rufe iyakokin bai yi wani tasiri ba.

Babu jihar Arewa da ke da ƙwararrun malamai kaso 50 – Babangida Aliyu

Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya bayyana cewa babu wata jiha a Arewancin Najeriya da ke da kaso 50 na ƙwararrun malamai.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron 22 Daily Trust karo na 22 da aka yi wa taken “Tsaron Abinci,” wanda aka gudanar a Abuja, a ranar Alhamis.

Aliyu, ya kuma soki matakin rufe iyakokin Najeriya, inda ya ce hakan bai haifar da komai ba face koma baya.

Ya yi kira ga Ma’aikatar Kiwon Dabbobi da ta haɗa kai da jami’o’in ilimi da noma don horas da manoma tare da bunƙasa samar da abinci.

“Me ake nufi da rufe iyakoki, alhali yawancin kayayyakin da ake samu a kasuwannin ECOWAS suna fitowa daga Najeriya?

“Kowace kasuwa ka shiga a ƙasashen nan, za ka tarar sama da rabin kayayyakin sun fito ne daga Najeriya,” in ji shi.

Ya kuma bayyana damuwarsa kan farashin dabbobi, inda ya kwatanta Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

“Misali, farashin shanu har yanzu ya fi arha a Nijar fiye da Najeriya.

“Wannan matsalar ta daɗe, tunda a baya ma mutane kan je can domin sayo shanu don yankawa ko bikin Sallah.”

Har ila yau, ya nuna damuwa kan ƙarancin ƙwararrun malamai a Arewancin Najeriya.

“Babu wata jiha a Arewa da ke da kaso 50 na ƙwararrun malamai da suka cancanta.

“Wannan yana shafar ingancin ilimin ɗalibai, bare waɗanda ba su samu damar zuwa makaranta ba. Gwamnatin Tarayya ta haɗa kai da jami’o’in noma da na ilimi don horas da mutane domin magance wannan matsala.”