Babu kasar da ta fi dacewa a zuba jari kamar Najeriya – dangote
Shugaban Kamfanin dangote Group Alhaji Aliko dangote ya ce babu wata kasa da ta fi dacewa a zuba jari a duniya fiye da Najeriya duk da matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.Ya bayyana hakan ne a lokacin da wakilan dillalan kasar nan suka kai masa ziyara a ofishinsa da ke Legas a ranar Lahadin da […]
Shugaban Kamfanin dangote Group Alhaji Aliko dangote ya ce babu wata kasa da ta fi dacewa a zuba jari a duniya fiye da Najeriya duk da matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da wakilan dillalan kasar nan suka kai masa ziyara a ofishinsa da ke Legas a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce: “Bai kamata mu yi kasa a gwiwa wajen bunkasa tattalin arzikinmu don matsalar tsaron da muke fuskanta ba. Bai kamata matsalar ta hana mu zuba jari ba, kasashen da ake ganin sun ci gaba ai su ma sun fuskanci irin wadannan matsalolin a baya, don haka ina so mu dauki matsalar tsaro a matsayin wani mataki da nan gaba za ta zame mana wata hanyar da za mu bunkasa tattalin arzikinmu.”
Ya ce duk da matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar nan, amma babu wata kasa da ta fi dacewa a zuba jari kamar Najeriya.