Babu kasar da ta jurewa yake-yaken basasa-Yakubu Gowon
Tsohon Shugaban Kasa, Janar Yakubu Gowon ya ce babu kasar da ta jurewa yake-yaken basasa saboda haka ya zama wajibi ’yan Najeriya su yi kishin kasarsu. Yakubu Gowon ya yi furucin ne yayin da yake jawabi a taron karawa juna sani da Cibiyar Tsaro ta shirya a jiya a birnin tarayya na Abuja. “Akwai manufa […]
Tsohon Shugaban Kasa, Janar Yakubu Gowon ya ce babu kasar da ta jurewa yake-yaken basasa saboda haka ya zama wajibi ’yan Najeriya su yi kishin kasarsu.
Yakubu Gowon ya yi furucin ne yayin da yake jawabi a taron karawa juna sani da Cibiyar Tsaro ta shirya a jiya a birnin tarayya na Abuja.
“Akwai manufa mai karfi a bambancinmu, saboda haka ya zama wajibi mu amince da bambancinmu don hadin kanmu. Ka da mu yarda da wani abu da zai sanya mutanen da ba su ji ba- ba su gani ba cikin matsala saboda bukatunmu na daban”. Inji shi
Da yake jawabin maraba a taron, Darakta Janar na Hukumar Jami’an Tsaron Farin Kaya na SSS, Lawal Daura ya ce hukumar za ta yi dukkan abinda za ta iya don tabbatar da zaman lafiyar kasar nan.
Ya gargadi kungiyoyi da wasu daidaikun mutane wadanda suke yin barazana da hadin kan kasar nan su nisanci haka don a cewarsa hadin kan kasar nan wata amana ce ta ke hannun hukumar.