Babu kotu ko caji ofis din da aka kai ni —Rahama Sadau

Rahama Sadau ta ce babu wata kotun Musulunci da ta yanke mata hukuncin dauri saboda batancin da wani ya yi a sanadiyyar hotunan da ta wallafa

Babu kotu ko caji ofis din da aka kai ni —Rahama Sadau

Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama Sadau ta ce babu wata kotun Musulunci da ta yanke mata hukuncin dauri saboda batancin da wani ya yi a sanadiyyar hotunan da ta wallafa.

Ta kuma ce labarin kanzon kurege ne cewa ’yan sanda sun gayyace ta ta amsa tambayoyi kan dambarwar batancin da hotunan nata suka jawo.

“Na samu sakonni cewa an tsare ni har kotu ta yanke min hukuncin dauri; ni ban san daga inda wannan jita-jita ta samo asali ba, don haka jama’a su yi watsi da ita”.

A makon jiya dai rahotanni da dama sun ce Rundunar ’Yan Sanda ta tsare Rahama kafin daga baya reshen jihar Kaduna na rundunar ya musanta, suna masu cewa gayyatar ta kawai suka yi ba tsarewa ba.

Sakon da jarumar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Talata ya ce, “Babu gayyatar da ’yan sanda suka yi min ko kotun da aka gurfanar da ni.

“Ina tabbatar wa masoya na cewa ina cikin aminci da koshin lafiya kuma ba a taba gurfanar da ni a gaban kotu ba; ina rokon masu neman amfani da abin da ya faru su yada karya su daina..!!!

A makon jiya wata majiyar ’yan sanda a Kaduna ta shaida wa Aminiya cewa Shugaban ’Yan Sandan Najerriya, Mohammed Adamu ne ya umarci Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya gudanar da bincike kan dambarwar da hotunan da jarumar ta wallafa suka haddasa.

Umarnin nasa na dakile yuwuwar fuskantar yamutsi na zuwa ne bayan takardar korafin da wani mutum ya rubuta a madadin al’ummar Musulmi saboda batancin da aka yi.

A makon jiya ne Rahama Sadau ta bayyana a wani bidiyo tana nadama tare lallashin al’ummar Musulmi game da abin da ya faru, wanda ta ce kaddara ce ta fada a kan hotunanta wadanda tuni ta cire su.

Jarumar ta kuma karyata labarun da ke yawo cewa an gurfanar da ita gaban Kotun Musulunci saboda batancin da wani mai sharhi a kan hotunan nata yi wa Manzon Allah (SAW).

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya