Babu laifi a tattauna da ’yan Boko Haram -Rotimi Paseda
Dan takarar kujerar gwamna a Jihar Ogun a karkashin jam’iyar UPN a zaben da ya gabata, wanda kuma shi ne Garkuwan Hausawan Jihar Ogun, Prince Rotimi Paseda ya shaida cewa ba laifi ba ne ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da ’yan ta’addar kungiyar Boko Haram domin samun maslaha.Ya ce shugaban na iya tattaunawa da […]
Dan takarar kujerar gwamna a Jihar Ogun a karkashin jam’iyar UPN a zaben da ya gabata, wanda kuma shi ne Garkuwan Hausawan Jihar Ogun, Prince Rotimi Paseda ya shaida cewa ba laifi ba ne ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da ’yan ta’addar kungiyar Boko Haram domin samun maslaha.
Ya ce shugaban na iya tattaunawa da ’yan kungiyar matukar yin hakan zai iya kawo dawwamammen zaman lafiya a kasar nan.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya bakunci taron da kungiyar ’yan jaridar Jihar Ogun ta shirya a jihar. A cewarsa, hatta kasashen da suka ci gaba sukan zauna taburin tattaunawa da ’yan ta’adda don neman maslaha a gefe guda kuma suna ci gaba da shirye-shiryensu na yakar ta’addacin. “Babu wani abin nuna damuwa idan aka zauna da ’yan Boko Haram domin neman matsaya.” Inji shi.
A karshe, ya yaba da gagarumar nasarar da sojojin Najeriya ke samu na yaki da ’yan ta’addar na Boko Haram, a sakamokon irin jajircewa da kyakkyawan shugabanci na Muhammadu Buhari.
A kwanakin baya ne Shugaba Buhari ya kara jaddada aniyar gwamnatinsa na son tattaunawa da ’yan Boko Haram, domin fahimtar da su yin watsi da ayyukan ta’addancin. Shugaban ya nuna yiwuwar tattaunawa da su duk da irin galabar da sojojin kasar ke ci a kansu. Shugaban ya bayyana hakan ne a sa’ilin da tawagar shuwagabannin addinin Kirista da sarakunan yankin birnin Abuja suka kai masa ziyarar gaisuwar Kirisimeti.