‘Babu laifi cire tallafin’

Wani mazaunin Kalaba ta jihar Kurosriba Alhaji AbdulWasi’u Wakas ya kare matakin da gwamnatin ta dauka inda ya ce, “Ni a nawa ra’ayin cire tallafi domin a bai wa ‘yan kasuwa damar shigo da man, matukar zai wadata, hakan babu laifi, domin kafin a cire tallafin ma man yana wahala, ana saye kan farashi daban-daban, […]

‘Babu laifi cire tallafin’
‘Babu laifi cire tallafin’

Wani mazaunin Kalaba ta jihar Kurosriba Alhaji AbdulWasi’u Wakas ya kare matakin da gwamnatin ta dauka inda ya ce, “Ni a nawa ra’ayin cire tallafi domin a bai wa ‘yan kasuwa damar shigo da man, matukar zai wadata, hakan babu laifi, domin kafin a cire tallafin ma man yana wahala, ana saye kan farashi daban-daban, kuma ko a kasuwar bayan fage kowanne da nasa farashin, ga wahalar bin layi kafin mutum ya samau man. Kuma tallafin ma ai wadansu tsirarun mutane ne ke amfana da shi, talaka na shan wahala. Amma idan aka yi hakuri komai zai wuce, domin da zarar an ce kowane dan kasuwa ya shigo da man za a samu gasa tsakani, dole su yi ragi, wanda ya fi arha shi mutane za su fi zuwa wurinsa suna saye.”
Ya ci gaba da cewa, wannan gwamnati ta fito fili ta ce a yi mata uzuri, a taimaka mata don ganin ta cim ma burinta, da tallafin man fetur din ma talaka bai fita a wahala ba, amma idan aka kyale kasuwa ta yi halinta duk wannan guna-guni da ake yi zai wuce.
Alhaji Wakas wanda dan kasuwa, ya ci gaba da cewa, “ Halin da tattalin arzikin kasa ya shiga ya sanya gwamnati daukar matakin, yanzu ga shi kungiyar kwadago ita kanta so take yi a yi wa ma’aikata karin albashi, don haka cire tallafin babu makawa zai taimaka wa gwamnati ta duba yiwuwar yin karin albashi, Magana ta gaskiya idan ‘yan Nijeriya suka kara hakuri, jin dadin zai zo nan gaba,’’ inji shi.

Daga Musa Kutama a Kalaba