Babu laifi don uba da ɗansa sun samu saɓani — Fubara

Gwamnan ya ce idan ma akwai matsala za su warware ta cikin sauki.

Babu laifi don uba da ɗansa sun samu saɓani — Fubara

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya nuna kwarin gwiwar cewa za a warware rikicin siyasa da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.

Ya ce babu laifi don uba da ɗansa su samu saɓani, inda ya jaddada cewa za a warware duka matsalolin da ke kasa.

Gwamnan ya yi magana ne a lokacin da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, ya jagoranci tawagar soji zuwa gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal, babban birnin jihar.

Fubara ya sake nanata kudurin shugaba Bola Tinubu na samar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan, musamman a lokacin zabe.

Gwamnan ya ce, “Ga jiharmu abar alfaharinmu, na san kowa yana mamakin abin da ke faruwa. Muna lafiya, babu matsala.

“Idan muna da batun cikin gida, za a warware shi kuma komai zai koma daidai.

“Babu wani laifi idan uba da ɗansa sun samu saɓani, idan akwai wata matsala, tabbas za mu warware matsalar.”

Tun da fari dai rikicin siyasa ya kunno kai a Ribas, lamarin da ya kai majalisar dokokin jihar kokarin tsige gwamnan.