Babu laifi idan na zama mataimakinyar shugaban kasa-Uwargidan Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya shirya tsaf domin ya zabi mace a matsayin mataimakiyarsa a wani taro na musamman da za su gudanar a wata mai zuwa. Uwargidan shugaban mai suna Grace ce ta sanar da hakan, inda ta kara da cewa babu wata matsala idan ta zama ita ce mataimakiyar mijin na ta. […]

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya shirya tsaf domin ya zabi mace a matsayin mataimakiyarsa a wani taro na musamman da za su gudanar a wata mai zuwa.
Uwargidan shugaban mai suna Grace ce ta sanar da hakan, inda ta kara da cewa babu wata matsala idan ta zama ita ce mataimakiyar mijin na ta.
Shi dai shugaba Mugabe, ya kasance mai jan ragamar mulkin kasar Zimbabwe tun lokacin da suka samu ‘yancin kai daga hannun turawa a shekarar 1980 zuwa yanzu.
Ya sha fada taruka cewa, sai lokacin da shi da jam’iyyarsa ta ZANU-PF suka ga ya dace ne zai yi
“Murabus” daga mulkin kasar.
Grace Mugabe ta shaidawa magoya bayan Jam’iyyar ZANU-PF ne a wani taro da ya gudana a birnin Bulawayo, inda ta ce za ayi gyara ga kundin tsarin jam’iyyar a cikin wata mai zuwa, inda zai ba shugaban kasar dama ya zabi mataimakiya mace.
“Mece ce matsalar idan na zama mataimakiyar shugaban kasa? Idan mutane sun san cewa ina aiki tukuru, kuma suna so su yi aiki da ni, shin akwai matsala a ciki?