Babu laifi malaman addini su riqa sa baki a harkokin siyasa – Sakataren CAN

Sakataren Qungiyar Kiristoci ta Qasa (CAN) reshen Jihar Bauchi, Rabaran Friday Vincent Bature ya ce babu laifi idan malaman addini su riqa sa bakinsu a harkokin siyasa sai dai kuma su riqa taka-tsantsan da masu mulki.Rabaran Bature ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Larabar […]

Babu laifi malaman addini su riqa sa baki a harkokin siyasa – Sakataren CAN
Babu laifi malaman addini su riqa sa baki a harkokin siyasa – Sakataren CAN

Sakataren Qungiyar Kiristoci ta Qasa (CAN) reshen Jihar Bauchi, Rabaran Friday Vincent Bature ya ce babu laifi idan malaman addini su riqa sa bakinsu a harkokin siyasa sai dai kuma su riqa taka-tsantsan da masu mulki.
Rabaran Bature ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Larabar makon jiya.
Rabaran Bature ya qara da cewa ya zamo wajibi a kan duk wani malamin addini a Najeriya idan ya ga masu mulki suna wasu abubuwa da suka sava wa doka ya je ya ba su shawari a sirrance domin duk shugaban da ya rasa masu ba shi shawari nagari, tabbas ya yi hasara duniya da Lahira kuma zai yi matuqar wahala ya yi nasara a shugabancinsa.
Ya ce duk lokacin da aka buga gangar siyasa ’yan siyasa suna zuwa wurin malaman addini domin neman albarka da goyon baya don haka malamai kowa ya san cewa malamai su ne fitilar haska al’umma a kowace qasa.
“Lokaci ya qure da malaman addini za su riqa qyamar ’yan siyasa domin xan siyasa yana mutunta duk wani malamin da ya sani yana da magoya baya a tsakanin al’umma,” inji shi.
Ya bayyana godiya ga Shugaban Qasa Muhammadu Buhari bisa matakin da gwamnatinsa ta fara xauka na magance matsalar tsaro kuma ya buqaci ya qara ba da fifiko wajen bunqasa harkokin noma, domin man fetur ba abu ne da zai xore ba.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da ba da goyon baya ga Shugaban Qasa domin ya zo da manufofi masu kyau na inganta rayuwar talakawan qasar nan.