Babu ma’aikacin da zai sake shiga ofis muddin bai yi rigakafin COVID-19 ba – Gwamnati
Gwamnatin ta ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar daya ga watan Disamba.
Gwamnatin Tarayya ta ce daga ranar daya ga watan Disamban 2021, babu ma’aikacin gwamnatin da za a sake bari ya shiga ofis, matukar bai yi rigakafin COVID-19 ba.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da COVID-19, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan yayin jawabin kwamitin a Abuja ranar Laraba.
A cewarsa, “Daga ranar daya ga watan Disamban 2021, za a bukaci dukkan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya su nuna shaidar yin rigakafin COVID-19, ko kuma takardar gwajin cutar da take nuna ba sa dauke da ita wacce ba ta wuce awa 72 ba, kafin su shiga ofisoshinsu a duk fadin Najeriya da ma ofisoshin jakadancinmu.
“Za mu fitar da bayanai kan hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da tsarin,” inji Boss Mustapha.
Ya ce alkaluman da aka samu a cikin wata hudu da suka wuce sun nuna cewa yawan kamuwa da cutar na raguwa a wasu Jihohin, yayin da yake karuwa a wasu.
Boss Mustapha ya ce ya zuwa yanzu, adadin mutanen da aka yi wa gwajin cutar sun kai 3,141,795.
Dangane da tsamin dangantaka kuwa tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a kan gwajin cutar, Mustapha ya ce an samu ci gaba matuka.
A watan Mayun da ya gabata ne dai gwamnatin ta hana matafiya daga kasashen Brazil da Indiya da kuma Turkiyya daga shigowa Najeriya saboda yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar a kasashen.