Babu mafaka ga barayin kasar nan a gwamnatina – Janar Buhari
dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari, ya ce idan ya zama Shugaban kasa babu yadda masu satar kudin jama’a za su shiga su sami mafaka a gwamnatinsa. Janar Buhari ya bayyana haka ne a garin Gombe a ranar Talata lokacin da jirgin yakin neman zabensa ya isa jihar. Ya ce […]
dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari, ya ce idan ya zama Shugaban kasa babu yadda masu satar kudin jama’a za su shiga su sami mafaka a gwamnatinsa.
Janar Buhari ya bayyana haka ne a garin Gombe a ranar Talata lokacin da jirgin yakin neman zabensa ya isa jihar.
Ya ce saboda rashin tsaro a kasar nan kowa yanzu yana ji a jikinsa domin an kashe kasa, babu wani
abu da yake tafiya daidai kowa ka tambaya sai ya ce maka jiki magayi.
Ya ce kashi 60 cikin 100 na al’ummar kasar nan matasa ne da suka je makaranta da wadanda ba su je ba, amma duk suna cikin mawuyacin hali na rashin aikin yi, kuma da zarar ya zama Shugaban kasa zai samar musu da aiki tare da inganta wutar lantarki da farfado da masana’antu.
Ya ce a baya tsakanin Kaduna da Kano da Ikeja da Asaba akwai masaku da suke ba ’yan Najeriya fiye da dubu 370 aikin yi, amma yanzu da kyar mutum dubu 30 suke aikin saboda babu wutar lantarki babu masana’antu.
Janar Buhari, ya yi alkawarin inganta ilimi da noma don ganin an samu karuwar matasa a harkar noma da zai sa su iya dogaro da kansu nan gaba.
Janar ya ce zai sanya salama a zukatan jami’an tsaro da kula da hakkokinsu da kuma ganin ya dawo da walwala a zukatan iyalansu.
Janar Buhari, ya yi kira ga jama’a su tabbata sun karbi katunan zabensu domin sai da katin ne za su iya zabarsa ya kawo canjin da aka dade ana nema a kasar nan.
Jiga-jigan Jam’iyyar APC da suka hada da shugabannin jam’iyyar na kasa da jagorar jam’iyyar a jihar Sanata danjuma Goje da dan takarar Gwamnan Jihar Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, sun yi jawabai masu kama hankali wajen gargadin magoya bayansu su guji tada hankali a lokacin zaben da ke tafe.
Taron gangamin ya gudana ne a filin wasa na Unguwar Pantami inda Shugaba Goodluck Jonathan, ya gudanar da nasa taron kuma an yi taron lafiya.