…Babu matsala – Hukumar Zabe

Sakamakon korafe-korafen da ake ta yi dangane da ingancin na’urar da ke tantancen katin zabe, hukumar zabe ta bakin mai magana da yawunta Nick Dazang ta bayyana babu wata matsala da za a samu dangane da amfani da wannan na’ura: Aminiya: Mene ne ingancin na’urar tantance katin zabe da kuka tsara yin amfani da ita […]

…Babu matsala – Hukumar Zabe

Sakamakon korafe-korafen da ake ta yi dangane da ingancin na’urar da ke tantancen katin zabe, hukumar zabe ta bakin mai magana da yawunta Nick Dazang ta bayyana babu wata matsala da za a samu dangane da amfani da wannan na’ura:

Aminiya: Mene ne ingancin na’urar tantance katin zabe da kuka tsara yin amfani da ita a lokacin zabe?

Nick Dazang: Muna da tabbacin ingancinta, saboda mun jarraba gwaji a kanta a lokuta da dama, kuma a jihohi daban daban, mun kuma samu sakamako mai karfafa gwiwa a game da ita. A ranar Asabar (gobe) in sha Allahu mun shirya tantance katin zabe na gwaji a jihohi 12 wanda zai kunshi jiha biyu ke nan a shiyyoyi shida na kasar nan. Za mu yi haka ne don kawar da fargabar masu tababa a game da ingancinta, kowa zai gani karara. Kuma a baya mun yi irin hakan ga ’yan majalisar dattawa wadanda suka kunshi ’yan jam’iyya mai mulki ta PDP da kuma ta adawa APC, inda suka bayyana gamsuwarsu da na’urar.
Aminiya: Ya ingancinta take a wajen rike caji, kasancewar akwai matsalar karancin wuta a yawancin wurare?
Nick Dazang: Baya ga kasancewarta na rike cajin wuta na tsawon awa goma sha biyu idan ana amfani da ita ba yankewa, mun tanadi janareta a dukkan cibiyoyin zabe da za a kai na’urar kamar yadda muka yi a lokacin zabe a shekara ta 2011, sannan kuma na’urar tana kashe kanta idan ta fahimci ba a amfani da ita don tsawaita lokacin rike cajin baturin da a ke amfani da shi, sannan akwai karin na’ura da za a ajiye a dukkan ciboyoyin zaben, baya ga wadanda ake amfani da su, don gudun shirin ko ta-kwana, wato ko da wadda ake amfani da ita ta samu tangarda sai a maye gurbinta da wacce ke ajiye.
Aminiya: Kamar mutane nawa ne ake da su a dukkan cibiyoyin zabe, sannan minti nawa ne zai dauki na’urar wajen tantance mutum guda?
Nick Dazang: Ba ta daukar fiye da minti guda wajen tantance mutum daya, kuma mun tsara cewa dukkan cibiyar zabe da ta dara mutum 750 za ta samu karin teburin tantance masu zabe da karin na’ura don magance cunkoso, kamar dai yadda muka yi a shekara ta 2011. dama mun so kirkiro karin cibiyoyin zabe a wurare masu matsalar cunkoso don saukaka wa al’umma, inda kuma majalisar kasa ba ta hana ba a lokacin da muka gabatar da bukatar, amma sai muka hakura da tsarin saboda cece-kucen da kudurin ya jawo, har sai nan gaba idan mun fadakar da jama’a sosai a kan al’amarin, saboda a yanzu haka akwai cibiyar kada kuri’a guda da ke da mutane sama da dubu biyu wani wajen ma har dubu uku a waje guda.