Babu matsala tsakanin Buhari da Kwankwaso – Kiri

Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa Alhaji Ado Sani Kiri ya ce babu wata matsala a tsakanin tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso saboda sha’awar manyan ’ya’yan jam’iyyar biyu na tsayawa takara Shugaban kasa a zabe mai zuwa.Alhaji Ado Sani Kiri ya bayyana haka ne ga […]

Babu matsala tsakanin Buhari da Kwankwaso – Kiri
Babu matsala tsakanin Buhari da Kwankwaso – Kiri

Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa Alhaji Ado Sani Kiri ya ce babu wata matsala a tsakanin tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso saboda sha’awar manyan ’ya’yan jam’iyyar biyu na tsayawa takara Shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Alhaji Ado Sani Kiri ya bayyana haka ne ga wakilinmu a Dutse, inda ya ce Janar Buhari da Gwamna Kwankwaso mutane ne da suka fahimci junansu ba su da wata matsala tare suke tafiya, wasu ne kawai suke baza jita-jita domin su haifar da rudani ga jam’iyyar kuma ba za su samu nasara ba.
Ya ce Najeriya tana bukatar mutane irin su Janar Buhari da Gwamna Kwankwaso, saboda fitar da ita daga mawuyacin halin da take ciki, inda ya bayyana Janar Buhari da magajin Sardauna shi kuma Gwamna Kwankwaso magajin Buhari.
Ya ce Jam’iyyar APC ta dauki matakin yin amfani da wakilan jam’iyyar wajen tsayar da ’yan takara domin magance amfani da kudi da haifar da rudani wajen neman takara a tsakanin masu sha’awar tsayawa takara.