Babu motar da ba zan iya satarta ba – Tsohon varawon mota

Da ka ganshi a cikin motarsa ba za ka yi tsammanin ya tava aikita wani mugun laifi ba, amma da ka yi hira da shi ya gaya maka cewa shi kasurgumin varawon mota ne a birnin tarayya na Abuja sai hankalinka ya tashi, to sai dai kuma da ka ji cewa yanzu ya tuba ya […]

Babu motar da ba zan iya satarta ba – Tsohon varawon mota
Babu motar da ba zan iya satarta ba – Tsohon varawon mota

Da ka ganshi a cikin motarsa ba za ka yi tsammanin ya tava aikita wani mugun laifi ba, amma da ka yi hira da shi ya gaya maka cewa shi kasurgumin varawon mota ne a birnin tarayya na Abuja sai hankalinka ya tashi, to sai dai kuma da ka ji cewa yanzu ya tuba ya zama mutumin kirki sai ka tausaya masa.
Shi dai Sam Aibaduan, dan asalin garin Uyo ne babban birnin jihar Akwa Ibom a yankin Kudu Maso Kudancin Najeriya, da ya kware wajen satar motocin alfarma a birnin tarayya na Abuja. Saboda ficen da ya yi wajen gano duk inda aka voye na’urar kulle mota ta sirri, abokansa suka sanya masa suna “Aljani”. To amma yanzu Sam ya tuba ya koma tukin motar haya inda yake tuka tasi a birnin tarayya Abuja. A yanzu ana kiransa Sam Direba.
Sam dan kimanin shekaru 37,  ya bayyana wa wakilin Aminiya a wata hira da suka yi a cikin motarsa a Abuja a cikin makon da muke ciki, cewa a lokacin da yake tashensa babu irin motar alfarmar da bai sata ba kuma ya sayar da ita ba tare da wata matsala ba. “A lokacin da nake tashe babu irin motar da ban sata ba kuma mota komai na’urar kulle ta da mai ita ya sanya mata zan iya gano inda take kuma na lalata ta.” Inji shi.
 Sam ya bayyana cewa,yana gano duk inda aka makala na’urar kulle mota da zarar ya kusance ta. Saboda haka sai ya bude ta ba tare da wata matsala ba cikin kankanin lokaci.
Sai dai kuma ya dage a kan cewa ba tsafi yake yi ba, baiwa ce kawai yake da ita ta gano sirrin mota, saboda ya tava koyon gyaran wayoyin wutar mota.
“Koyon gyaran wayoyin mota da na tava yi shi ne ya ba ni kwarewa ta musamman wajen budewa tare da gano duk inda aka voye na’urar kulle mota cikin kankanin lokaci. Amma wadansu da yawa daga cikin abokaina suna zaton cewa tsafi nake yin amfani da shi wajen gano na’urar mota.” Inji shi.
Ya kara da cewa gungunsu ba su kwana a cikin gida mai jama’a, sai dai gidajen da ba a kammala ba saboda kada a sirinsu ya tonu.
Ya bayyana cewa yana da wani aboki ana kiransa Gambo, dan asalin jihar Kano da ya kware wajen tukin mota, shi yake tuka duk motar da suka sata zuwa kasuwar da za su sayar da ita.
Ya ce sukan sayar da motocin ba a jihohin da suka sace su ba, misali motar Abuja suna sayar da ita a Legas, ta Legas kuma su sayar a Kano.“Ba ma kwana a cikin gida mai jama’a sai dai gidajen da ba a kammala ba don kada asirinmu ya tonu. Wani lokaci ma a karkashin gada ko kuma mu kwana a wuraren da ake sayar da kayan maye.”  Inji shi.
Sai dai kuma Sam ya ce asirinsa ya tonu ne lokacin da ya saci motar wani jami’an SSS a Abuja. “Mota ce kirar Siyana ta zamani, wacce take da talabijin a gaba da bayanta. Gaskiya na so motar nan sosai saboda ban tava ganin irinta ba. Mun ganta ne a cikin Asokoro. Motar ta bani wahala kafin in gano inda aka voye na’urar kulleta ta sirri. A lokacin sai na gaya wa abokina cewa zan je in sayar da ita in kawo masa kasonsa, amma daga bisani sai na wuce da ita garinmu Uyo. Ashe ban sani ba an kama abokina Gambo har sun karvi lambar waya ta. Ni ban san cewa motar ta jami’an SSS ba ce,  sai suka kira ni a waya suka ba shi ya ce mani in zo akwai harka ga shi ya zo Uyo. Duk da cewa jikina ya ba ni cewa akwai matsala, amma da yake tsautsayi ba ya wuce ranarsa sai na taho inda ya ce mu hadu.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa yana zuwa sai wata kyakkawar budurwa ta nufo shi ta tambaye shi ya yi mata kwatancen wata unguwa, amma yana cikin ba ta amsa sai kawai ya ga wadansu mutane sun kewaye shi sun kama shi cikin ruwan sanyi.
Sai dai kuma Sam ya yaba wa jami’an SSS saboda abin da ya kira kula da hakkinsa tare da ba shi abinci mai kyau a inda suka kulle shi.
Ya bayyana cewa sakamakon satar mota ya tava zama a gidan yari na Kuje da ke Abuja, kuma an sha kai shi ofishin ’yan sanda da kotu amma saboda yana da wadanda suke tsaya masa sai a sallame shi. “An  sha kama ni, na tava zama gidan kurkuku na Kuje saboda satar mota, amma kuma duk lokacin da aka kama ni ina da mutanen da suke tsaya mani a sallame ni.” Inji shi.
Sam wanda ya ki yarda a dauki hotonsa, ya dage a kan cewa ba zai bayyana sunayen mutanen da suke tsaya masa a duk lokacin da ya shiga matsala a lokacin yana satar mota ba.Amma ya ce tun lokacin da jami’an tsaro na hukumar SSS suka kama shi ne shiriya ta zo masa.
“Na tuba ne tun lokacin ina tsare a hannun jami’an SSS a Abuja. Na yi tunani na ga cewa rayuwata tana cikin kunci kodayaushe. Gashi ina samun kudi amma ba zan iya fitowa in yi walwala ba kamar yadda sauran jama’a suke yi. Kuma na yi tunani na ga cewa sata ba ta da riba. Za ka saci motar miliyoyi Naira amma a ba ka kudi kadan wanda bai kai rabin kudin da aka sayi motar ba.” Inji shi.
Sam ya bayyana cewa a yanzu ya zama direban tasi yana samun abin rufa wa kansa asiri ta halastacciyar hanya. “Yanzu na fi jin dadin rayuwata. Ina neman halaliyata, ina walwala ba na jin tsoro.Saboda haka ina kira ga varayi su tuba su koma ga Allah za su fi jin dadin rayuwarsu.”
Sam ya bayyana cewa yana shirin yin aure ya zauna tare da iyalinsa cikin kwanciyar hankali da lumana.