Babu niyyar janye tallafin man fetur a yanzu – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da niyyar cire tallafin da take bayarwa a bangaren shigowa da man fetur daga kasashen ketare. Ministar Kudi Hajiya Zainab Ahmad ce ta bayyana haka a taron hadin gwiwa a tsakanin Bankin Duniya da na Hukumar  Lamuni ta Duniya (IMF) na bana da ya gudana a Amurka. Hajiya Zainab […]

Babu niyyar janye tallafin man fetur a yanzu – Gwamnati

Minisitar Kuxi Hajiya Zainab Ahmed

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da niyyar cire tallafin da take bayarwa a bangaren shigowa da man fetur daga kasashen ketare.

Ministar Kudi Hajiya Zainab Ahmad ce ta bayyana haka a taron hadin gwiwa a tsakanin Bankin Duniya da na Hukumar  Lamuni ta Duniya (IMF) na bana da ya gudana a Amurka.

Hajiya Zainab Ahmad ta ce “Shawarar da Hukumar IMF ta ba Najeriya na ta janye tallafin da take bayarwa a bangaren man fetur don a yi amfani da kudin wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka abu ne mai kyau, amma a halin yanzu hakan ba zai yiwu a kasar nan ba.”

A yayin taron masana tattalin arzikin duniya da ya gudana a Amurka, Hukumar IMF ta ba Najeriya shawarar muddin tana son tattalin arzikinta ya habaka to sai ta janye tallafin da take bayarwa a bangaren man fetur.

Jim kadan da bayar da wannan shawarar ce masana  harkar tattalin arzikin duniya suka bayyana ra’ayoyinsu.  A yayin da wadansu suka yi maraba da shawarar, wadansu suna ganin hakan ba zai yiwu a wannan lokaci da Najeriya take fuskantar tabarbarewar tattalin arziki ba.

Sai dai Hajiya Zainab Ahmad ta ce shirye-shirye sun yi nisa a tsakanin Najeriya da Bankin Duniya don karbo bashin Dala biliyan daya domin bunkasa bangaren samar da wutar lantarki da bangaren noma da samar da tsabtataccen ruwan sha a kasar nan. Ta ce wannan bashi yana kunshe ne da kudin ruwa mai sauki inda kasar  za ta dade tana cin gajiyarsa ba tare da ta ji a jiki wajen biya ba.

Rahotanni sun ce an fara samun dogayen layin mai a wasu jihohin kasar nan bayan da Hukumar IMF ta ba Najeriya shawarar ta janye tallafin da take ba bangaren man fetur.

Sai dai tuni Kamfanin Man fetur na Kasa (NNPC) ya kwantar da hankalin jama’a inda ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da shirin janye tallafin a wannan lokaci, kuma akwai wadataccen man fetur don haka babu dalilin da zai sa jama’a suka rika fargabar za a samu karancin man fetur a wannan lokaci.

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno

An ceto ma’aikacin INEC da aka yi garkuwa a Zamfara

Za a gurfanar da mutum biyu don shan taba a jirgin sama

Mutum 4 sun maƙale, an ceto 3 bayan gini ya rufta a Kano