Babu ranar amincewa da kasafin kudi- Majalisar Dattijai

Majalisar Dattawa jiya ta sake jaddada cewa ba ta tsayar da ranar amincewa da kudurin kasafin kudin shekarar 2018.   Shugaba Muhammadu Buhari ya mika kasafin kudin a ranar 7 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata.   Hakan shi ne karo na biyu da majalisar ta ce ba ta tsayar da ranar da zartar […]

Babu ranar amincewa da kasafin kudi- Majalisar Dattijai

Majalisar Dattawa jiya ta sake jaddada cewa ba ta tsayar da ranar amincewa da kudurin kasafin kudin shekarar 2018.
 
Shugaba Muhammadu Buhari ya mika kasafin kudin a ranar 7 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata.
 
Hakan shi ne karo na biyu da majalisar ta ce ba ta tsayar da ranar da zartar da kasafin kudin bana ba.
 
Buhari ya gabatar da kasafin kudin ne da wuri wata guda da gabatar da kasafin kudin shekarar 2016 da shekarar 2017.
 
Mai magana da yawun majalisar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi dan jam;iyyar APC daga jihar Neja ya fada wa manema labarai cewa “Tuni aka fara gudanar da batun kasafin kudin amma ba zan iya fadar ranar da za a kammala ba. Muna aiki sosai a kai kuma muna baiwa ’yan Najeriya tabbaci a karshe dai za mu samu kasafin kudin da zai amfani ’yan Najeriya”.