…Babu ruwanmu da shirin – Gwamnatin Taraba
Sanarwa da gwamnatin jihar Taraba ta fitar cewa ita ba ta bai wa gwamnatin tarayya fili don samar da wuraren kiwo a jihar ba ya nuna irin yadda gwamnatin jihar ke nuna kyama ga fulani makiyaya.Sanarwar wanda mai taimaka wa gwamnan jihar na musamman ta fuskar watsa labarai Mista Silbanus Giwa ya bayar, ta nuna […]
Sanarwa da gwamnatin jihar Taraba ta fitar cewa ita ba ta bai wa gwamnatin tarayya fili don samar da wuraren kiwo a jihar ba ya nuna irin yadda gwamnatin jihar ke nuna kyama ga fulani makiyaya.
Sanarwar wanda mai taimaka wa gwamnan jihar na musamman ta fuskar watsa labarai Mista Silbanus Giwa ya bayar, ta nuna cewa gwamnatin jihar ta Taraba ba ta taba zama da jami’an ma’aikatar gona ta tarayya ba kan magana samar da filaye don samar da makiyayar dabbobi, balle a ce ta bai wa gwamnati fili don wannan aiki.
Jihar ta Taraba dai ta fi kowace jiha a kasar nan yawan shanu da albarkatun dabbobi, wanda a wata kididdiga da aka yi aka nuna cewa akwai sama da shanu miliyan bakwai tare da tumaki da yawan su ya haura miliyan uku.
Kamar yadda bincike ya nuna, akwai manyan kasuwannin shanu har guda shida a jihar, inda ake sayar da shanu sama da dubu 4 a duk mako.
Binciken ya kuma numa cewa, gwamnatin jihar ta Taraba na samun miliyoyin Naira ta fuskar harajin da ake karba daga jangali da kuma wurin masu saye da sayar da shanu a jihar.
Manyan kasuwannin shanu a jihar sun hada da ta garurruwan Mayo- Ndaga da Ngouroje da Maihula, da Garba –Chede da Iware da Tella da kuma sauran wadansu kanana kasuwannin shanu a sassa daban-da ban na jihar.
Har wa yau kuma a yankin Mambilla akwai sama da shanu miliyan hudu. Wannan yanki ana ganin cewa ya fi kowane shashi na kasar nan albarkatun dabbobi. Makiyaya a jihar, kamar yadda bincike ya nuna, suna fuskantan matsaloli masu yawan gaske, amma gwamnati ba ta dauki wani mataki don magance matsalolin ba
A cikin wata hira da shugaban Miyetti- Allah reshen jihar Taraba, Malam Sahabi Tukur, ya bayyana cewa makiyaya ba su yi mamakin sanarwa da gwamnatin jihar ta bayar kan cewa ba za ta ba gwamnatin tarayya fili don shirin ta na samar da wuraren kiwon dabbobi a jihar ba. Ya ce gwamnatin jihar ba ta son ganin fulani makiyaya a jihar kuma idan ma da gwamnatin za ta samu dama to za ta ce fulani makiyaya su fice daga jihar. A cewar shugaban Miyetti –Allah, kungiyarsu ta nemi ganin gwamnan jihar Mista Darius Ishaku don su bayyana wa gwamnati wadansu abubuwa dangane da makiyaya, amma gwamnan ya ki yarda ya gansu.
Ya ce a jihar ta Taraba barayin shanu sun kashe sama da makiyaya 200, sa’annan kuma suka sace shanu fiye da Dubu 20, amma ba wani abu da gwamnati ta yi. Ya ce har yanzu ana cigaba da satar shanu, musaman a yankinWukari da Gassol da Bali da Donga kuma ana kashe makiyaya, amma ba wanda ya kula da wannan hali da makiyaya ke fuskanta.
Malam Sahabi Tukur ya yi zargin cewa, wasu ne ke zuga gwamnan jihar da kada ya yarda ya yi hulda da makiyaya, wannan shi ya sa a kasafi kudin jihar na wannan shekarar ko kwabo gwamnanti ba ta ware don sashin kiwon dabbobi ba.
Ya kara da cewa, amma abin mamaki gwamnatin jihar ta ware sama da Naira miliyan 600 don bunkasa kiwon kifi a cikin kasafin kudin ta na wannan shekarar.
Wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa akwai wuraren da gwamnatocin baya suka samar a jihar har guda 42 don kiwon dabbobi kuma 9 daga cikin wadannan filayen har ma gwamnati ta yi doka a kansu, watau”Gazatted grazing Reserbes.’
Shugaban na Miyyetti –Allah ya bayyana cewa, jihar ta Taraba za ta iya samar da wani bangare na madara da nama mai yawan gaske ga kasar nan idan gwamnati ta inganta albarkatun dabbobi da Allah Ya bai wa jihar. Amma sabo da kiyayyar da gwamnatin jihar ta Taraba ke nuna wa fulani makiyayya an kasa mai da hankali wajen bunkasa kiwon shanu a jihar.
kungiyar ta Miyyetti –Allah ta ce akwai bukatar gwamnatin Tarayya ta kafa ma’aikatar sarrafa madara da nama a jihar don rage kudaden da ake kashewa wajen shigowa da Nama da madara daga kasashen waje.