Babu ruwanmu da siyasar Najeriya – ’Yan Nijar

Shugaban al’ummar kasar Nijar mazauna Kasuwar Alabar Rago a Jihar Legas, Alhaji Habibu dandauda Alaramma, ya ja kunnen mutanen kasarsa su guji tsoma kansu cikin harkokin siyasar Najeriya domin ba huruminsu ba ne. Ya ce, “Dole ne mutanenmu su kiyaye daga yin rajista ko jefa kuri’a a zabe, wanda lamari ne da ya shafi ’yan […]

Babu ruwanmu da siyasar Najeriya – ’Yan Nijar
Babu ruwanmu da siyasar Najeriya – ’Yan Nijar

Shugaban al’ummar kasar Nijar mazauna Kasuwar Alabar Rago a Jihar Legas, Alhaji Habibu dandauda Alaramma, ya ja kunnen mutanen kasarsa su guji tsoma kansu cikin harkokin siyasar Najeriya domin ba huruminsu ba ne. Ya ce, “Dole ne mutanenmu su kiyaye daga yin rajista ko jefa kuri’a a zabe, wanda lamari ne da ya shafi ’yan Najeriya kadai.
Alhaji Habibu dandauda ya fadi haka ne cikin hira da wakilinmu jim kadan bayan kammala taron tattaunawa a kan al’amuran siyasar kasashen biyu da kungiyar ta gudanar a ofishinta a ranar Talata. Ya gargadi mutanensa da su yi nesa daga shiga harkokin zabe na Najeriya domin kauce wa haifar da rudani a tsakanin kasashen biyu.
Ya ce, duk da yake akwai dadaddiya kuma kyakkyawar dangantaka a tsakanin al’ummomin Najeriya da Nijar, al’amarin siyasar mulkin kowace kasa ya sha bamban. “Saboda haka a matsayinmu na shugabanni dole ne mu fadakar da mutanenmu muhimmancin kauce wa shiga al’amuran da ba su shafe su ba. A matsayinmu na baki kamata ya yi dukkanmu mu tashi tsaye wajen yin addu’o’in Allah Ya sa a yi zaben Najeriya lami lafiya. Idan wani dan kasar Nijar yana da sha’awar yin siyasa, to ya saurara zuwa nan da dan lokaci kadan da za mu fito a nan Najeriya mu zabi ’yan majalisar dokokin kasarmu ba tare da mun koma gida ba. Wannan garabasa ce da gwamnatin Shugaba Muhammadou Issoufou ta amshi rokon da muka dade muna yi na a ba mu damar kada kuri’unmu daga kasashen da muke zaune,” inji shi.
Alhaji Habibu dandauda, ya yi kira ga ’yan kasar Nijar da ke zaune a Najeriya su fito su karbi takardu domi tabbatar da yawansu kuma su samu wakilin da zai wakilce su a harkokin mulkin kasarsu. “Wannan abin jinjina wa ne ga Shugaba Muhammadou Issoufou, wanda shi ne shugaba na farko da ya bayar da irin wannan dama ga ’yan kasarsa da ke zaune a kasashen duniya su shiga harkokin tafiyar da mulkin dimkradiyya,” inji shi.
Alhaji Habibu dandauda, ya ce ya kamata gwamnatin Nijar ta fito da salon sanin muhimmancin mutanenta da ke zaune a kasashen duniya domin yin haka ne zai karfafa musu gwiwar sanin irin gudunmawar da za su bayar ta fannin ci gaban kasarsu.