Babu saɓani tsakanin Tinubu da Shettima – Fadar Shugaban Ƙasa

Hadimin ya ce labarin ƙazon kurege ne, wanda babu gaskiya a cikinsa.

Babu saɓani tsakanin Tinubu da Shettima – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata jita-jitar samun saɓani tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.

Mataimakin Shettima na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai, Stanley Nkwocha, ya bayyana cewa mataimakin shugaban ƙasa na da matuƙar muhimmanci a gwamnatin Tinubu.

Nkwocha, ya ce jita-jitar rashin jituwa tsakanin shugabannin biyu ba gaskiya ba ce.

Ya jaddada cewa Shettima yana da aminci tare da samun cikakken haɗin kan gwamnati.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar murnar cikar Shettima shekara 58, Nkwocha ya ƙaryata jita-jitar.

Ya bayyana ta a matsayin magana mara tushe, inda ya ce shugabannin biyu suna zaune ƙalau tare da ganin mutuncin juna.

Har wa yau, ya ce Shettima yana da cikakken goyon bayan Shugaba Tinubu.

Ya ƙaryata batun cewar Tinubu ya ajiye Shettima a gefe ba ya tafiya da shi cikin al’amuran gwamnatinsa.

Ya ƙara da cewa Shettima yana tallafa wa gwamnatin Tinubu fiye da yadda kowa ke tsammani.

Nkwocha ya yaba wa Shettima saboda ƙwarewar da ya nuna wajen ci gaban gwamnatinsu.

Ya ce hikimar da tsohon gwamnan na Borno, ke nunawa, sun taimaka wajen tabbatuwar shirye-shiryen Tinubu na inganta Najeriya.