‘Babu sabani tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Kano’
Gwamnatin Kano ta ce babu bambanci tsakaninta da gwamnatin tarayya a kan dokar kulle a jihar. Gwamnatin jihar ta Kano dai ta sassauta dokar har ta ba da damar Sallar Juma’a da ta Idi tana cewa ta yi hakan ne don saukaka wa alummar jihar halin da suka samu kansu a ciki sakamakon yaduwar annobar […]
Gwamnatin Kano ta ce babu bambanci tsakaninta da gwamnatin tarayya a kan dokar kulle a jihar.
Gwamnatin jihar ta Kano dai ta sassauta dokar har ta ba da damar Sallar Juma’a da ta Idi tana cewa ta yi hakan ne don saukaka wa alummar jihar halin da suka samu kansu a ciki sakamakon yaduwar annobar coronavirus.
Tun da farko dai gwamnatin tarayya, ta bakin Kwamitin Shugban Kasa Mai Yaki da Annobar COVID-19, ta kara wa’adin dokar zaman gidan da makonni biyu a jihar.
Wannan lamari dai ya jawo rudani, inda wasu ke ganin akwai tufka da warwara a tsakanin gwamnatocin biyu game da yakin da ake yi da annobar.
- ‘Sassauta dokar kulle a Kano ka iya jawo matsala a Najeriya’
- Ganduje ya yarda a yi sallar Idi da ta Juma’a a Kano
Sai dai Kwamishinan Yada Labarai Kwamared Muhammad Garba ya ce babu wani bambanci tsakanin matsayar gwamnatocin biyu domin ita ma gwamnatin jihar tana bin dokar kullen, illa kawai sassauta dokar da ta yi.
‘Gwamnati ta yi tsare-tsare’
Ya kuma ce gwamnatin ta fitar da wasu tsare tsare da za a bi wajen saukaka kullen.
Malam Muhammadu Garba ya bayyana cewa bayan tattaunawa da malamai da jami’an kiwon lafiya da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnati ta dauki matakin saukaka wa alummar jihar kwanaki uku na dokar wato ranakun Lahadi da Jumaa da kuma Laraba daga karfe 10 zuwa karfe 2 ta yadda jama’ar jihar za su samu saukin sa’o’i 12 a mako.
Kwamushinan ya kuma jaddada cewa duk da gwamnatin ta sahale wa alumar jihar gudanar da sallar Idi, ta soke bukukuwan Sallah a dukkanin masarautun jihar guda biyar.
Har ila yau gwamnatin ta kafa wani kwamiti da zai kula da raba kayayyakin kariya da suka hada da sabulun wankin hannu da man tsaftace hannu da takunkumin fuska a masallatan Juma’a da ke jihar tare da tabbatar da cewa jama’a sun yi amfani da shawarwarin likitoci na bayar da tazara da sanya takunkumi da kuma wankin hannu.
Majalisar malamai ta yi korafi
Tuni dai Majalisar Malaman jihar, ta bakin shugabanta, Shaikh Ibrahim Khalil, ta soki matakin gwamnatin.
A wata hira da ya yi da BBC, malamin ya ce kamata ya yi gwamnatin ta yi nazari mai zurfi kafin ta yanke hukunci a kan lamarin.
Ya kuma ce duk da ba ta tuntubi majalisar malaman ba, da gwamnatin ta yi la’akari da bukatun mutane, sannan ya ce duk wanda yake jin idan ya je masallaci zai kamu da cutar, ko kuma ba ya jin dadain jikinsa, to zai iya zamansa a gida.