Babu sabani tsakanina da Gwamna Badaru – Nakudu

Sanata Sabo Muhammad Nakudu ya musanta jita-jitar da wadansu ke yadawa cewa ya samu sabani tsakaninsa da Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Abubakar Badaru saboda ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar kujerar Gwamnan Jihar a zaben shekarar 2019. Sanata Sabo Nakudu ya musanta wannan jita-jita ce a wata hira da ya yi da manema labarai a […]

Babu sabani tsakanina da Gwamna Badaru – Nakudu
Babu sabani tsakanina da Gwamna Badaru – Nakudu

Sanata Sabo Muhammad Nakudu ya musanta jita-jitar da wadansu ke yadawa cewa ya samu sabani tsakaninsa da Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Abubakar Badaru saboda ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar kujerar Gwamnan Jihar a zaben shekarar 2019. Sanata Sabo Nakudu ya musanta wannan jita-jita ce a wata hira da ya yi da manema labarai a Dutse a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce batun tsayawa takara ta kowane irin mukami bai gabansa, a tattara a kai kasuwa ba ya bukata kuma ya bukaci masu son jin kwakwaf su tambayi Gwamna Badaru domin karin haske.
An zargi Sanata Nakudu da ganawa da wadansu jami’an gwamnatin Badaru a Kano a gidan wani na hannun damar Gwamnan don neman goyan bayansu, sai dai Nakudu ya ce babu gaskiya a wannan batu, karya ce kawai da wasu ke kitsawa domin haifar da fitina a cikin tafiyar gwamnati mai ci.
Sanata Nakudu ya ce bai taba zama da kwamishinonin Gwamna Badaru ko wadansu jami’an gwamnatinsa a Kano ko a wani wuri ba, kuma ba ya da burin tsayawa takara, wannan ma da yake rike da shi Allah yake roko Ya sa ya sauka lafiya.
Da ya juya kan harkar mulkin kasar nan, Sanata Nakudu, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta dauki mataki mai tsauri a kan mayakan Neja-Delta da suke fasa bututun mai. Ya ce hakan ya zama dole domin magance barazanar da ’yan ta’addan Neja-Delta suke yi kamar yadda ta murkushe Maitasine da mayakan Boko Haram.
Ya nuna damuwarsa kan yadda shugabannin gwamnatin PDP suka lalata kasar nan a tsawon shekara 16 da suka yi suna mulki, inda ya zargi jam’iyyar da halatta cin hanci a kasar nan har ya yi karfin da ke neman zama wata annoba a kasar.