Babu sabuwar PDP a Gombe -Habu Mu’azu
Alhaji Habu Mu’azu shi ne tsohon shugaban matasan Jam’iyyar PDP na Jihar Gombe a zamanin Gwamna Muhammad danjuma Goje, sai dai kuma sakamakon raba-gari da suka yi da ubangidan nasa, yanzu yana sahun gaba na masu adawa da Sanata Goje. A tattaunawarsa da manema labarai a Gombe ya musanta samuwar Sabuwar PDP a jihar duk […]
Alhaji Habu Mu’azu shi ne tsohon shugaban matasan Jam’iyyar PDP na Jihar Gombe a zamanin Gwamna Muhammad danjuma Goje, sai dai kuma sakamakon raba-gari da suka yi da ubangidan nasa, yanzu yana sahun gaba na masu adawa da Sanata Goje. A tattaunawarsa da manema labarai a Gombe ya musanta samuwar Sabuwar PDP a jihar duk da cewa Sanata Goje ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa shi dan sabuwar PDP ne:
Me ya sa mafi yawan ku ’yan Jam’iyyar PDP kuke ganin za a iya magance matsalarta, kuma ko a Gombe akwai sabuwar PDP?
Ni dai na san akwai matsalolin cikin gida da suka dabaibaye Jam’iyyar PDP kamar yadda kowa ya sani, amma wannan ba wata matsala ba ce da za ta raba kan PDP. Idan za a iya tunawa a shekara ta 2003 gwamnonin PDP sun yi bore cewa ba za su zabi Obasanjo ba Atiku Abubakar za su zaba, amma cikin kankanen lokaci aka shawo kan matsalar komai ya koma daidai suka dawo suka zabi Obasanjo. Matsalar wancan lokaci ta fi ta yanzu saboda duk gwamnonin suna goyon bayan Atiku Abubakar ne shi ya sa idan ka duba wannan matsalar ba komai ba ce. A nan Gombe kuma ni ban ga wata sabuwar PDP ba, gaskiya a matsayina na dan siyasa amma wata kila ku da yake ’yan jarida ne kun gani ko kuna da labari amma da kun ce min akwai APC zan ce muku akwai, amma sabuwar PDP kan babu ita a Gombe idan kuma akwai ta, ina ne ofishinsu yake kuma wane ne shugabanta.
A wata hira da ’yan jarida suka yi da wani tsohon dan majalisar jihar Alhaji Usman Shabuki, ya ce akwai sabuwar PDP a Gombe kuma Sanata danjuma Goje, shi ne jagoranta me za ka ce a kan wannan?
Abin da zan ce shi ne na san Goje yana PDP amma Akhaji Shabuki ba dan PDP ba ne, bai taba zama dan PDP ba, domin lokacin da ya yi takarar dan majalisa ma ba a PDP ya yi ba a AD ne a 1999, sannan a shekarar 2011 ya sake yin takara ne a Jam’ iyyar ANPP, shi ne ma kodinetanta yaushe ya canja sheka ya dawo PDP. Na san Shabuki sosai bai taba zama dan PDP ba, idan danjuma Goje zai bugi kirji a matsayinsa na Sanata ya yi magana a gaban Majalisar Dattawa ya ce shi dan sabuwar PDP ne wannan daban, amma Shabuki ba dan PDP ba ne. Shi ma Goje sai dai ya tsaya a iya majalisar amma ba a Gombe ba, ina kuma tabbatar muku cewa babu wanda zai bi Goje zuwa sabuwar PDP a Gombe.
Akwai jita-jitar cewa a karamar Hukumar Akko mazabar da Sanata Goje ya fito an kori wasu ’ya’yan Jam’iyyar PDP saboda sun shiga sabuwar PDP me za ka ce a kan hakan?
Ba gaskiya ba ne, ita Jam’iyyar PDP babu wanda ta kora don ya shiga sabuwar PDP yanzu, don ina tsohuwar PDP ba na sabuwar sai a ce an kore ni su dai ba cikakkun ’ya’yan PDP ba ne, watakila suna wata jam’iyya ce daban domin sabuwar PDP da suka fito suna neman a san su ne shi ya sa suke kiran ’yan jarida suke fade-fade.
Wasu ’yan siyasar yankin Arewa ba sa kaunar ganin sake tsayawar takarar Shugaba Goodluck Jonathan a 2015, me za ka iya cewa a kai?
Kowa na iya fadin albarkacin bakinsa sai dai wani abu a kasar ne shi ne idan yau an ce ba a kaunar Goodluck Jonathan, babu wani dan Arewa da zai iya cin zabe ba tare da goyon bayan ’yan Kudu ba. Haka su ma ’yan Kudu babu yadda za a yi su iya cin zabe ba tare da goyon bayan ’yan Arewa ba, idan kuma kai Musulmi ne dole sai ka hada kai da Kirista haka Kirista dole sai ya hada kai da Musulmi domin babu yadda za a yi mutum ya ci zabe da kuri’un Musulmi ko Kirista zalla.
Yanzu kai wa kake goya wa baya?
Jam’ iyyar PDP mana, domin ni cikakken dan Jam’iyyar PDP ne dole in goyi bayan PDP da kuma shugaban da zai kawo mana canji a wannan kasar.
A shekara ta 2015 wa za ka mara wa baya a Jihar Gombe?
Gwamna dankwmabo zan marawa, yana aiki a Jihar Gombe, ba ni da wani dalilin da ba zan mara masa baya ba. Saboda a gaskiya yana aikin da ya kamata kuma shugaba ne wanda ya san mutuncin jama’arsa duk da ma dai ba na masa shigshigi a mulkinsa kuma ba na bukatar kowane irin matsayi a gwamnatinsa ko kwangila, amma dai yana yi wa talakawansa abin da ya kamata kuma dankwambo Gwamna ne da ba ya sa a je a kona gidan wani ko a sare kafar wani.
Wace shawara kake da ita ga gwamnonin nan bakwai da ake kira G-7?
Ba na jin na kai in iya ba su kowace irin shawara saboda sun fini sani da kwarewa a harkar siyasa kuma suna da dalilansu, sannan suna da wata bukatarsu da suke son ta biya da idan ba a PDP suke ba, babu yadda za a yi su iya samun biyan bukatarsu.