Babu sauran abin da Buhari zai iya tsinana wa Najeriya —Kwankwaso
Kwankwaso ya ce kame-kamen da Buhari ke yi ya nanu babu wani abin da gwamantinsa za ta iya yi kan matsalar tsaro.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce babu wani abin da gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari za ta tsinana wa ’yan Najeriya a kan sha’anin tsaro.
Kwankwaso wanda tsohon ministan tsaro ne, ya zargi Gwamnatin Buhari da yin shakulatun-bangaro da matsalar sha’anin tsaro a Najeriya.
- Gwamnati ta fara ‘tattaunawa’ da wadanda suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna
- Garkuwa da dalibai mafiya muni 10 bayan na Chibok
“Na san duk wani soja ko wani mutum da ke hulda da sojoji zai yi makaki kuma zai damu kan halin (rashin tsaron) da kasar nan take ciki,” inji Kwankwaso wanda yanzu shi ne Jagoran Jam’iyyar NNPP.
Da yake tattaunawa da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a, Jagoran na NNPP, ya ce bai taba tunanin cewa sha’anin tsaro a Najeriya zai yi irin tabarbarewar da ya yi a halin yanzu ba.
A cewarsa, bayanin da Gwamnatin Buhari take yi cewa tana yin bakin kokarinta na cire wa ’yan Najeriya kitse a wuta a bangaren tsaro alhali matsalar sai karuwa take yi, ya nanu karara cewa babu wani abin da gwamantin za ta iya yi a bangaren tsaro.
Sai dai ya bayyana cewa babban zaben 2023 ’yan Najeriya za su yi wa kansu kiyamullaili su wancakalar da gwamnatin Jam’iyyar APC domin samun sabuwar Najeriyar da suke fata.
Ya ce ’yan Najeriya sun kai makura kan kamun ludayin gwamantin mai ci, wanda ba su yi zato ba, don haka babu yadda za a yi su yarda gwamnatin jam’iyyar APC ta ci gaba da jan ragamar kasar.
Sakaci da sha’anin tsaro
“Dukkanmu mun san da labarin harin jirgin kasan Kaduna, wanda da ma jirgin kasan ne kadai abin da ya rage matafiya suke bi tare da tabbacin tsaro domin su isa Kaduna daga nan su karasa zuwa wasu wurare.
“Mutane sun sha gargadin cewa za a iya kai wa jirgin hari amma aka yi biris da su.
“Ga shi yanzu an kashe mutane an yi garkuwa da wasu, kuma Allah kadai Ya san halin da suke ciki.
“Ko maganar a zo a gani game da yadda za a kubutar da wadanda aka yi garkuwa da sun ba sa yi.”
Muhimmancin sha’anin tsaro
“Ya kamata gwamnati ta bayar da muhimmanci ga sha’anin tsaro, domin a matsayin tsohon ministan tsaro ban taba tunanin cewa yanayin tsaron Najeriya zai taba tabarbarewa haka ba cikin dan kankanin lokaci.
“Wani lokaci nakan ce, ‘wai ya aka yi al’amarin tsaron kasar nan ya lalace haka?’
“Amma kamar yadda muka sani ne, rashin shugabanci na gari shi ne babbar matsalarmu,” a cewar Kwankwaso.
Ya yi zargin cewa shugabannin siyasa a kasar a yanzu ba su da karfin ba wa sojoji kwarin gwiwa da sauran abubuwan da suka dace na horo da makamai da kayan aiki da kuma kulawa domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
A cewarsa, tun da har APC ta kasa samar wa ’yan Najeriya shugabanci nagari, da alama jam’iyyarsa ta NNPP ce ta karbe shugabancin kasar daga APC a 2023.