Babu sauran sasantawa tsakaninmu da ‘yan bindiga – Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce yarjejeniyar da gwamnatinsa ta sanya wa hannu ta sasantawa da ‘yan bindiga ta rushe. A ranar 28 ga watan Agustan bara ne dai gwamnan ya tattauna tare da sanya hannu a kan yarjejeniyar yin afuwa da wakilan ‘yan bindigar da suke ci gaba da cin karensu ba […]

Babu sauran sasantawa tsakaninmu da ‘yan bindiga – Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce yarjejeniyar da gwamnatinsa ta sanya wa hannu ta sasantawa da ‘yan bindiga ta rushe.

A ranar 28 ga watan Agustan bara ne dai gwamnan ya tattauna tare da sanya hannu a kan yarjejeniyar yin afuwa da wakilan ‘yan bindigar da suke ci gaba da cin karensu ba babbaka a kananan hukumomi takwas na jihar.

Masari, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC ranar Laraba, ya ce daukar matakin ya biyo bayan kin mutunta yarjejeniyar da ‘yan bindigar suka yi.

Gwamnan ya ce a cikin yarjejeniyar da suka saka wa hannu tun da farko, ‘yan bindigar sun amince su ajiye makamansu tare da barin yankin Arewa Maso Yamma kwata-kwata.

Rahotanni dai sun nuna ko a ‘yan kwanakin nan ‘yan bindigar sun kai wasu munanan hare-hare da su ka yi sanadiyyar rayuka da kuma dukiyoyin alu’ummar jihar da dama.

Masari ya ce, “Mun yanke shawarar tattaunawa da ‘yan bindigar tun da farko ne saboda mu kaurace wa asarar rayuka da dukiyoyi, amma hakar mu ta gaza cimma ruwa, saboda haka yanzu mun yanke hukuncin damka ragamar a hannun jami’an tsaro don yin abin da ya kamata.

“A kokarinmu na mutunta dokar, mun janye dukkan jami’an tsaron sa-kai da ‘yan kato-da-gora don mu bar ‘yan bindigar su ci gaba da walwala”, in ji gwamnan.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar wa jihar isassun jami’an tsaro don ta samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar daga jihar.

Ban da jihar ta Katsina, a lokuta da dama gwamnonin jihohin Arewa Maso Yamma sun sha tattaunawa a kan yadda za su kawo karshen matsalar a yankin nasu.

Idan dai za a iya tunawa ko a ranar 16 ga watan Mayun da ya gabata sai da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin Najeriya umarnin yin barin wuta a kan ‘yan bindigar da suka addabi jihar, wacce ita ce jiharsa ta asali.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos