Babu shaida

Wani dan sanda ne ya kama danladi a dakin bahayar wani otel, ya same shi da kullin tabar wiwi guda uku. Ga yadda ta kwashe a tsakaninsu: danladi: “Ba ni da laifi, a kullum na zo dakin bahayar nan, idan na nemi kore su sai kawai in ga sun fada aljihuna. Abin kamar na jinnu.” […]

Babu shaida
Babu shaida

Wani dan sanda ne ya kama danladi a dakin bahayar wani otel, ya same shi da kullin tabar wiwi guda uku. Ga yadda ta kwashe a tsakaninsu: danladi: “Ba ni da laifi, a kullum na zo dakin bahayar nan, idan na nemi kore su sai kawai in ga sun fada aljihuna. Abin kamar na jinnu.” dan sanda: “Ka dauke ni wawa ne, kana son in amince da wannan karyar?” danladi: “Bari in tabbatar maka da gaskiyata.” dan sanda ya mika wa danladi wiwin da ya kwace daga wurinsa, ya ce masa: “To tabbatar mani, in gani.” Koda danladi ya amsa sai ya zuba su a tukunyar kora kashi, ya danna ruwa suka bace. Ganin haka sai dan sanda ya ce: “To, nuna mani aljihunka in ga yadda wiwi ta koma. Shi kuwa danladi ya ce: “Wace wiwi kuma?” Daga nan ne dai dan sanda ya fahimta ashe wayau ya yi masa. Ga shi yanzu bai da damar kama shi, tun da babu shaida.
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08098157899

An gano baƙin haure 30 a ɓoye cikin tankar mai a Turkiyya

An tsare ɗan gwagwarmaya kan sukar gwamnatin sojin Nijar

Alhazan Kebbi rukunin farko sun dawo gida

Rukunin farko na Alhazan Kebbi 426 sun dawo gida