Babu shugaban da zai iya kawar da ’yan bindiga a 2023 —Lai Mohammed

Lai Mohammed ya ce ko Shugaba Buhari ba shi da tabbacin kawo karshen ’yan bindiga a shekara mai zuwa.

Babu shugaban da zai iya kawar da ’yan bindiga a 2023 —Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Raa Al’adu, Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce babu wani shugaba da zai ce zai iya kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a shekara mai zuwa.

Ministan ya yi wannan martani bayan an tambaye shi a wani taron manema labarai cewa ko kalubalen tsaron da ake fuskanta a halin yanzu zai kare kafin Shugaba Buhari ya sauka daga mulki a 2023.

Lai Mohammed ya ce ba ya tsammani ko shugaba Buhari ba shi da tabbacin cewar za a iya murkushe ayyukan ’yan bindiga a shekara mai zuwa.

Ministan ya musanta zargin da ake wa Shugaba Buhari na rashin katabus wajen kare rayukan al’umma da ake kashewa kusan kullum.

Idan ba a manta ba, tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa Buhari ya yi iya kokarinsa, babu wani abin da zai iya tabukawa fiye da hakan a nan gaba.

Matsalar tsaro da ta yi kamari musamman a yankin Arewacin Najeriya, inda ta sa mutane da dama fusata har aka shiga yi wa Shugaba Buhari zanga-zanga, don kawo karshen zubar da jinin al’umma da ake yi a yankin.